✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawi Modu: An kama dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo

Sojoji sun kama kasurgumin dan Boko Haram Modu Yawi a hanyar Damboa, Jihar Borno.

Sojojin Najeriya sun kama wani babban dan kungiyar Boko Haram, Yawi Modu, wanda suke nema ruwa a jallo.

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabsa sun kama Yawi Modu ne a kan hanyar Damboa zuwa Wajiroko.

Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Onyema Nwachukwu, ya sanar a Abuja ranar a Alhamis cewa sojoji sun kwace abubuwan fashewa masu tarin yawa a wata cibiyar hada abubuwan fashewar Boko Haram a Karamar Hukumar Damboa ta Jihar Borno da kuma Gushua a Jihar Yobe.

Ya kara da cewa sojoji sun tarwatsa masu sayar wa kungiyar ta Boko Haram kayan hadin abubwan fashewar Boko Haram.