Daily Trust Aminiya - Yaya kuke ganin wasikar da Obasanjo ya rubuta wa Buhari?
Subscribe

Mohammed Dan Ali Shugaban Miyetti Allah na Kebbi

Yaya kuke ganin wasikar da Obasanjo ya rubuta wa Buhari?

Wasikar da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya sake rubuta wa Buhari ta haifar da cece-kuce mai yawa da kuma tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin al’ummar kasar nan. Obasanjo ya sha rubuta wasiku yana cacccakar kowace gwamati, kusan daukacin shugabannin kasar nan in aka cire Shonikan da Janar Abdulsalami, duk ya rubuta musu irin wannan wasika. Wakilanmu sun nemi jin ra’ayin jama’a kan wasikar inda suka ce:

Nuna kiyayya ce kawai – Alhaji Usman Adamu

Daga John D. Wada, Lafiya

Ni dai a nawa ra’ayi wannan wasika ta tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ga sHUGABA Muhammadu Buhari yana nuna kiyayyarsa ce karara ba ga Shugaba Buhari kadai ba har da ci gaban Arewacin kasar nan da al’ummarta baki daya. Don kamar yadda ka sani babu kasar da ba ta fuskantar irin nata kalubalen tsaro. Don me zai rika fitowa yana bayyana wa duniya cewa laifin Buhari ne duk da cewa shi ma a lokacinsa an fuskanci irin wadannan matsaloli. Shi ya sa dole ’yan Arewa mu hada kai musamman a wannan lokaci da wadansu tsofaffin shugabannin kasar nan irin su Obasanjo ke sa mana ido.

Ya sa ni kowace kasa tana da nata matsalolin – Alhaji A.Mohammed

Daga John D. Wada, Lafiya

A gaskiya ya kamata Obasanjo ya gane cewa kowace  kasa tana da irin nata matsalar tsaro da take fuskanta. Ba sabon abu ba ne. Kuma batun Fulani makiyaya ina so ya gane cewa dokar kasar nan ta bai wa kowane dan kasa damar zama a duk inda ya ga dama a kasar nan. Saboda haka a ganina abin da ya kamata ’yan Najeriya baki daya musamman shugabanninmu su yi a wannan lokaci na jarrabawa shi ne mu hada hannu mu nemi mafita maimakon mu ci gaba da zargin junanmu bayan mun san nauyi ne da ya rataya a wuyan mu duka.

Borin kunya ne kawai –Dan Ali

Daga Bashir Lawal Zakka Birnin Kebbi

Ni yadda nake gani wasikar nan da tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Buhari,  kowa ya san Obasanjo ya san shi ne da cin mutuncin shugaban da yake mulki, domin kowa ya san Obasanjo shi ya kawo marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa da Jonathan, amma dukkansu babu wanda bai rubuta wa irin wannan wasika ta cin mutunci ba. Don haka ba wani sabon abu ba ne, domin wadanda ya kawo kan mulki ma ba su tsira ba, ballatana wanda yake adawa da shi, Kuma Obasanjo yana  ganin babu wanda ya iya mulki sai shi, don haka duk wadannan rubuce-rubuce da ya yi wa Buhari babu komai illa borin kunya ne kawai.

Adawa ce kawai ta siyasa – Umar Yakubu Hassan

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Wannan abin da tsohon Shugaban Kasa, Obasanjo ya yi sam bai kamata ba. Shi a kullum burinsa ya nuna kowa bai iya ba sai shi, adawa ce kawai ta siyasa domin a matsayinsa na tsohon Shugaban Kasa kuma yake son a yi gyara, ai abin da ya kamata ya yi shi ne yana iya zuwa ya samu Buhari ya ba shi shawarwari kan yadda za a gyara al’amuran kasar na da su ne suka bata. Kuma alhakin hakan yana bisa wuyansu, don haka ya fito yana kalubalantar gwamnatinsa, wannan ba gyara yake son a yi ba kiyayya ce kawai.

Ta yi daidai sai dai akwai kuskure – Adamu Mu’azu Tela

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Wasikar da Obasanjo ya aike wa Shugaba Buhari ta yi daidai, amma akwai inda ya yi kuskure da ya danganta abin ga wata kabila. Don ya bayyana kuskure a kan yadda Buhari yake tafiyar da mulkinsa ya yi daidai domin a gyara. Amma don an yi wani abu a cikin kasa wanda yake na wani yanayi na hargitsi wanda ya danganta shi ga wata kabila, sam wannan bai dace ba ko kadan. Kuma a ra’ayina ta kowacce hanya Obasanjo ya aike wa Buhari sako ya yi daidai.

Obasanjo gani yake ya fi kowa iya mulki –Abubakar Umar

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

Shi Obasanjo gani yake ya fi kowa iya mulki a duk kasar nan. Don haka wannan wasika tasa tana iya haddasa tashin hankali a kasar nan idan aka yi la’akari da irin kalaman da ta kunsa, domin babu komai a cikinta illa son kai da rashin kishin kasa wanda shi ne dalilin da ya sa Obasanjo yake yin irin wadannan rubuce-rubecen nasa. Da irin wannan wasika ne ya sa Obasanjo ya taba shiga gidan yari a lokacin marigayi Janar Abacha. Ni dai a ra’ayina wannan wasika da ita da shirme duk daya suke.

More Stories