✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaya maza suke ji in suka ga mata da ‘A Cuci Maza’?

Yaya maza suke ji idan suka gano irin wadannan kayan ba na gaskiya ba ne?

A Cuci Maza, wani salon kwalliya ne da mata ke ta hanyar amfani da kayan karya don kara musu kyau, ta yadda za su ja hankalin maza, su ga sun birge su.

To sai dai yaya mazan suke ji idan suka gano irin wadannan kayan ba na gaskiya ba ne?

Aminiya ta tattauna da wasu maza don jin ra’ayinsu game da mata da suka amfani da A Cuci Maza.

Hassan Bello, wani matashi, ya ce duk macen da ta hada wani abin da ba da shi aka halicce ta ba, ta aikata ba daidai ba.

A cewarsa, “Gara ta fito inda Allah ya halicce ta, idan namiji ya gan ta, in yana son ta a haka, shi ke nan ya karbe ta. In kuma ba irin macen da yake so ba ce ya hakura domin  in ta yaudare shi ya aure ta zai iya samun matsala bayan aure.

“Shari’ar addinin Musulunci ta ba da damar in ma namiji ya auri mace amma daga bisani ya ga abubuwan da ba haka ya san su ba, an ba shi damar ya rabu da ita.

“Akwai cikakken bayani a Suratul Bakarah, to shi ya sa yaudara baki daya ba abar da ake son mutum ya sa a gaba ba ce. Don haka A Cuci Maza yaudara ce,” inji shi.

Shi kuwa wani magidanci, Adamu Abubakar, ya ce lamarin ya taba faruwa da abokinsa.

“Abokina ya taba ganin wata yarinya wacce yanayin tsawon gashinta ya birge shi, suka yi magana har suka yi aure.

“Bayan sun yi auren, sai ya ce bari ya je ya yi wanka, ita ma ta  ce bari ta watsa ruwa, sai ya ce kafin ta fito daga bayi zai je ya siyo musu abin da za su ci, amma har ya je ya dawo ba ta fito daga bayin ba.

“Sai bayan wasu mintuna ta fito sai ya ga abin da ba shi ya yi tsammani ba. Sai ya rasa abin da zai yi, ta tambaye shi mene ne ya ce mata ba komai, sai ya yi mata wayo ya ce ai ya yi mantuwa ne a waje.  A haka ya baro ta a dakin tana ta jiran shi bai dawo ba.

“Irin wannan abin yana faruwa kuma bai kamata ba. kowa da abin da yake birge shi; wasu fuska, wasu gashi, wasu kuma yanayin jiki. Ina da mata a gida in kuwa har zan kara aure yanzu, na fi son mace mai jiki sosai saboda matata ba da kiba gaskiya,” inji Adamu Abubakar.

Sai dai ya ce a cikin mazan ma ana samun wasu suna kara wani abin a jikinsu, kamar gemu da gashi, inda su ma suke kiran shi da A Cuci Mata.

Bashir Shehu kuwa shi da zuciya daya yake son mace, kuma ko me za ta, sai dai son nata ya kan ragu idan ya gano ta saka wani abin kari a jikinta daga bisani.

Shi kuwa wani mai suna Gambo Ishaku cewa ya yi, “In dai ina son mace na ga tsarin jikinta ya yi min, amma daga baya na gano cewa tana karawa da wani abin, to zai dame ni na wani lokaci kuma zan nuna mata ya dame ni, amma dole  na hakura tun da ina son ta, dole mu ci gaba.” daga inda muka tsaya kawai zan nuna mata cewa abun da yi ba daidai bane.