✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaya zan yi a matsayina na sabon ango?

Me ya sa yawancin amare ba su cika yarda da mazansu ba a farkon aure.

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko.

Tambaya: Na karanta shafinki na Jaridar Aminiya inda wani ya turo da tambayar yi wa matan aure fyade.

A matsayina na wanda yake shirin yin aure, an ce yawancin amare ba su cika yarda da mazansu ba a farkon aure koda suna son junansu, wannan ya sa wadansu suke fada musu da karf, shin hakan ma laifi ne ko kuwa?

Amsa: Hakan ai shi ya fi zama laifi saboda ya cutar, saboda tsananin zafin ibadar aure a karon farko ga budurwa, ko tana so ma sai ta sha wahala ina kuma ga ba ta so?

Kuma wata daga wannan fyaden ranar farkon ne sai ta ji ta tsani ibadar aure har ta koma ga Mahaliccinta ba za ta taba kaunatarsa ba balle ta more.

Mafi muhimmancin abin da ya sa hakan ya zama laifi shi ne don ba haka shari’a ta tanada ba.

Abin da ya dace a ilimantar da yarinya ilimin ibadar aure tun kafin zuwan daren farko, shi kuma ango ya hada da hakuri ya yi ta rarrashi da dabaru da jan hankali har ya samu hakarsa ta cim-ma ruwa.

Amma yi wa sabuwar amarya ibadar aure da kokawa tana ihu tabbas cin zarafi da rashin sanin mutuncin ta ne.

Tambaya: Anty Nabila ki kara gaya wa maza cewa danne wa mata hakkinsu da yin hulda da su kamar daya daga cikin kadarorinsu ne da suka mallaka ba daidai ba ne.

Su sani ko ta yaya suka huldace su, su abokan rayuwarsu ne kuma daidai suke wajen hakkoki kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana a cikin Alkur’ani Mai girma. -Daga wanda ya san darajar ’ya mace.

Tambaya: Anty Nabila na yi auren farko na yi wasa da igiyar aurena saboda a lokacin haukar yarinta tana kaina ban san darajar aure ba.

Bayan zawarcin shekara biyu yanzu na kusa tarewa a gidan miji, wace shawara za ki ba ni kan dabarun da ke kike amfani da su kuma kika ga tasirinsu a cikin huldodinki na yau da kullum?

Amsa: To Allah Ya ba da zaman lafiya Ya hada kawunanku da alheri, amin.

Ga shawarwarin Anty Nabilah: 1. Addu’a takobin mu’umini, kada ki ji kunya ko nauyi, kada ki manta kada ki kasa tambayar dukkan bukatunki komai kankantarsu daga wajen Allah (Subhanahu Wa Ta’ala).

Idan kin shiga matsala kafin wani ya ji Allah za ki gaya wa, ko girki ne ki kasance mai rokon Allah Ya sa abincin da zan dafa a yau ya yi dadi daidai irin dadin da zai gamsar da kuma burge maigidana.

Allah Ka sa in ya ci kuma ya yaba mani da sauransu.

Kuma ko gishiri kike bukata, kafin ki nema a wurin kowa nema a wurin Allah. Nana A’isha (RA) an ruwaito tana umartar jama’a da su roki dukkan bukatu daga wajen Allah Madaukakin komai kankantarsu.

Don haka ko ni’imar ibadar aure kike nema kafin ki sayi hakkin maye ki gaya wa Allah, Shi ya halitta ’ya mace kuma Ya ba ta ni’imar, in Allah Ya amshi addu’arki ni’imar da zai ba ki ba wani maganin mata ko hakkin mayen da zai iya ba ki ita.

2. Ba cuta ba cutarwa: In har ba ki so a cuce ki kada ki cuci kowa, kowa ki ba shi hakakinsa da martabarsa, in kina haka kowane irin tuggu za a kulla maki da sannu zai warware ba tare da ya yi wani tasiri a kanki ba.

3. Aure ibada ne, don haka kamar yadda ake daurewa da dagewa a yi Sallah da sauran ibadoji a cikin lokacinsu, to haka ma ayyukan cikin gidan aure komai a tashi a yi shi a cikin lokacinsa.

To, da haka za ki ga komai yana tafiya daidai a rayuwar aurenki, amma in kina kara’in abubuwan rayuwar aure to a hankali za su cukuikuye maki wanda hakan na iya durkusar da aurenki.

Sai mako na gaba insha Allah da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.