✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Ya’yan Babban Alkalin Najeriya 2 sun lashe zaben fid-da-gwani a Bauchi

Daya daga cikin ’ya’yan Babban Alkalin ya lashe zaben ba tare da hamayya ba.

‘Ya’yan Babban Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko, sun lashe zaben fitar da gwani na ‘yan Majalisar Tarayya a Jihar Bauchi .

Daya daga cikinsu mai suna Sirajo Ibrahim Tanko, ya nemi takara kuma ya lashe zaben fid-da-gwani a Bauchi ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC don neman zuwa Majalisar Dattijai.

Suraj ya yi galaba ce a kan dan majalisa mai wakiltar yankin a yanzu, Sanata Adamu Bulkachuwa.

Wakilan jam’iyyar APC sun zabi Suraj Ibrahim Tanko, da kuri’u 189 yayin da Ibrahim Baba Imba ya samu kuri’u 177, sai Sanata Adamu Bulkachuwa wanda bai samu kuri’a ko daya ba.

Haka kuma akwai wani dan Babban Akalin mai suna Sani Ibrahim Tanko, da ya lashe zaben fid-da-gwani na jam’iyyar PDP na dan Majalisar Wakilai ta tarayya na mazabar Shira Giade ba tare da hamayya ba.