✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin Kaduna: Jami’an tsaro sun bude Sakatariyar Gwamnati

Jami’an tsaro sun balla kwadon da NLC ta sanya da nufin tababtar da yajin aiki.

An kwashi ’yan kallo tsakanin jami’an tsaro da Kungiyar Kwadago da Kasa (NLC) a yayin yajin da NLC ke yi kan korar ma’aikata da Gwamantin Jihar Kaduna ke yi.

Tun da sanyin safiya NLC ta isa sakatariyar Gwamnatin Jihar, ta sanya kwallo ta kulle shi domin tabbatar da ganin ta cimma burinta da gurgunta aikin gwamnati a Jihar a yayin yajin aikin.

Shugaban NLC na Kasa, Ayuba Wabba na tsaka da yi wa taron ma’aikata jawabi a Sakatariyar Kungiyar ne jami’an tsaro suka balla kwadon Kungiyar, suka bude sakatariyar suka kuma ci gaba da sintiri.

Yanayin ya sanya ma’aikata cikin tsaka mai wuya game da abin da zai iya biyo baya idan suka shiga Sakatariyar, wanda hakan ya sa suka yi cirko-cirko a gaban sakatariyar.

Aminiya ta gano jami’an tsaron da suka yi dafifi suna kula da kofar shiga sakatariyar sun hada da ’yan sanda, ’yan banga, jami’an Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) da Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Kaduna (KASTELEA).