✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

YBN da 13×13: Yadda siyasa ke neman raba kan Kannywood

A yayin da zaben 2023 ke matsowa, alamu sun nuna akwai baraka a tsakanin masu fada-a-ji a Kannywood

’Yan Kannywood sun dade suna bayyana cewa za su shiga siyasa a dama da su domin su samu damar gogayya da masu rike da madafun iko domin su kawo wa masana’antar ci-gaba.

Sai dai a daidai lokacin da zaben 2023 ke kunno kai, alamu sun fara nuna akwai baraka a tsakanin masu ruwa da tsaki a masana’antar ta fuskar siyasa.

A makon jiya ne darakta Falalu Dorayi ya wallafa wani dogon rubutu da ya sanya wa suna tsakanin YBN da 13×13, inda a ciki ya ce, “A mahangata, duk kungiyoyin suna aiki ne kusan iri daya: Taimakon mutanen masana’antar da mutanen wajanta. Wannan abu ne da idanu suka gani suka tabbatar.

“Shawara ce domin masalaha. Kar ku ba wa shaidan dama wajen shiga tsakaninku, kuma kar ku ba wa zuciya dama ta jefa muku gaba ko kiyayya.

“Ku yi komai domin Allah. Kar ku ba da gurbin haibaici tsakaninku.

“Ku nuna dattako ku ci gaba da samar da alheri da yada shi a tsakanin mabukuta.”

Falalu ya kara da cewa, “Abin alfahari, Kannywood ta hada ku cikin sana’a kafin zuwan kungiyoyin.

“Abokan juna ne ku sana’arku daya, wajen zamanku daya kuna kwana guri daya tare.

“Kun ci abinci tare a kwano daya, hakan ya nuna da kauna da zumunci da abota; Duk wata alfarma da arziki da yake tare da mu mun same shi sanadiyar Kannywood.

“Me zai hana ku mai da hankali wajen godiya ga Allah da ci gaba da taimakon da kuka saba, maimakon kokarin ba wa shaidan dama ya haifar da gaba.

“Da kaunar juna muka zo duk inda muke, da kaunar juna ne za mu wuce inda muke a yanzu.

“Ina rokon jagororin kungiyoyin, ina gama ku da Allah ku yi duba da alheran da kuke raba wa da farin ciki da suke saka wa a zukata masu yawa, ku yi aiki da hankali kar ku bari shaidan ya haifar da gaba da habaici tsakaninku.”

Kungiyar 13×13

13×13 kungiya ce ta mawaka da ’yan fim da ta hada su Dauda Kahutu Rarara da Adam A. Zango da Aminu Ala da Nura M. Inuwa da Umar M. Shareef da Yakubu Mohammed da Fati Nijar da Aishatu Humaira da sauransu.

A wata sanarwar da suka fitar, sun ce kungiyar ba ta siyasa ba ce, inda suke ce kungiya ce ta taimakon kai-da-kai da taimakon mabukata.

Aminiya ta gano cewa a cikin kungiyar akwai wadanda suke tallata PDP da wadanda suka tallata APC a zaben wancan lokaci.

A kwanakin baya sun kai ziyara wajen Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, inda suka nuna masa goyon bayansu, har suka raira masa wasu baitoci.

Kungiyar YBN

Ita YBN an samu sunan ne daga sunan Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello sai aka kara ‘Network’, kuma tana karkashin jagorancin Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ne.

Sun yi wa Yahaya Bello da Musa Halilu Dujiman Adamawa da Aisha Buhari wakoki da dama, sannan kuma suna tallata Yahaya Bello a matsayin dan takarar Shugaban Kasa.

Yaushe aka fara samun barakar?

A bara aka yi wata ’yar takaddama bayan furodusa Abdul Amart Maikwashewa ya yi taron bikin karrama gwarazan gasar wakar Garkuwan Matasa, wadda mawakan Kannywood suka yi wa Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, inda aka raba kyautar motoci da babura da sauransu.

Sannan bayan kyaututtukan wakar, Abdul Amart ya raba wa jarumai irin su Bello Mohammed Bello da sauransu.

Shi ma Dauda Kahutu Rarawa ya sa gasar rawa ta wakar Dogara ya dawo, wadda ya rera wa tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara a lokacin da ya dawo Jam’iyyar APC daga PDP.

An raba kyaututtukan motoci da KEKE-Napep da sauransu ga wadanda suka samu nasara.

Sannan Rarara din ya ba wasu jarumai irin su Tijjani Asase da Jamila Nagudu da Sadiya Sosai da sauransu motoci.

Bayan taron karrama wadanda suka yi nasara a gasar da Abdul Amart ya sa, sai Khalid Yusuf Ata, daya daga cikin manyan yaran Ali Nuhu ya yi rubutu a kan Abdul Amart, inda yake cewa, “Ba ka nuna ka fi kowa komai ba, a hakan ka faranta wa kowa…

“Sun dade suna ba za ka iya ba, amma suna ji suna gani Allah Ya iya maka!”

A karshe ya ce, “Allah Ya maka tsari da ’yan kiran lamba. Kwashewa farin cikin al’ummar masa’antar shirya finafinai.”

A kasan rubutun nasa sai wasu suka yi ta jan hankalinsa a kan cewa habaici babu kyau.

Shi ma darakta Sanusi Oscar 442 ya wallafa wani hoton rubutu a wancan lokacin mai dauke da cewa, “Ba don Abdul Amart ba, da yanzu ’yan Kannywood mabarata ne.”

Sannan ya rubuta cewa, “Wannan ra’ayina ne, ku biyo ni a sannu za ku ji dalilin da ya sa na rubuta haka.”

A kasan rubutunsa, Hamza Talle Maifata ya ce, “Ina daya daga ciki.”

Shi ma Garzali Miko ya ce, “Haka yake ko shakka babu,” sannan furodusa Abdulaziz Dan Small ya ce, “Ba karya ba ne, haka abin yake.”

A wani bangaren kuma, Darakta Aminu S. Bono ya wallafa wani dogon rubutu, wanda ya yi na daya da na biyu, inda a ciki ya yaba tare da kawo wasu hanyoyi da dama da mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya bi domin kawo sauyi a masana’antar Kannywood.

Kwatsam sai Mansur Make Up wanda na kusa da Adam A. Zango ne sosai ya wallafa cewa, “Rayuwar ’yan fim ta shiga rudani. Wannan ya ce ba don wane ba da harkar ta lalace, wannan ma ya fadi nasa gwanin.”

Sannan ya rubuta cewa, “Kuma babban abin damuwar ita ce in fa ba ka yi hakan ba wai ba ka cikin manya a bangaren da kake yabo, kuma ba su san wannan habaice-habaicen ba ne ya kashe fim din tun farko…”

A kasan rubutun ne darakta, Aminu S. Bono, makusancin Rarara ya rubuta cewa, “Mansur ni ban yi rubutu don ce-ce-ku-ce ba, na yi domin karin karfin gwiwa ga kowane bangare ne saboda ni na san amfaninsu, amma wasu suna amfani da haka don cin mutuncin wasu, ba daidai ba ne wannan.

“Mutane da Allah Ya ba mu suke taimakon masana’antar mu yi musu addu’a tare da fatan samun irinsu da yawa nan gaba, shi ke nan fa rubutuna kuma a ciki na yabi kowane bangare, saboda ko’ina na amfana da su kuma sun amfanar.”

Sai wani mai amfani da sunan Garkwan_Abdulamarta ya mayar wa Aminu S. Bono da martani cewa, “…ka tsargu ke nan?”

Haka aka yi a zabukan baya?

Aminiya ta ruwaito a shekarar 2015 Kannywood ta rabu biyu kan ’yan Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da ’yan Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP a wancan lokacin.

A lokacin akwai kungiyar All Progressibes Congress (APC) Northern Musicians Forum (ANMFO) da ke goyon bayan Buhari; Akwai kuam Kannywood Initiatibe Door-2-Door for Atiku 2019 da ke goyon bayan.

Wadanda suka goyi bayan Atiku a kungiyar ta wancan lokacin su ne Mika’il Bin Hassan (Gidigo) wanda shi ne kodineta da Sani Danja da Fati Muhammad da Zaharaddeen Sani da Usman Mu’azu da Ummi Zee-Zee da Salisu Mu’azu da Mustapha Naburaska da mawaki Abubakar Sani da sauransu.

’Yan kungiyar ANMFO da ke goyon bayan Buhari kuma su ne mawaki Dauda Kahutu Rarara da Yusuf Haruna (Baban Chinedu) da Adam A. Zango da Bello Muhammad Bello da Fati Nijar da Abdul Amart (Mai Kwashewa) da Halima Atete da Jamila Nagudu da Aminu Ladan Abubakar (ALA) da Rukayya Dawayya da sauransu.

A lokacin, an yi wakar ‘Lema ta yage’ karkashin jagorancin Abdul Amart, inda a ciki akwai Rarara da wasu da dama da ke cikin tafiyar 13×13 a yanzu.

Sai dai daga baya duk kungiyoyi sun samu sabani a tsakaninsu, inda da yawansu suka fito fili suka rika caccakar junansu.

A zaben 2019 ma haka aka yi, inda aka samu sabani har wasu daga cikin ’yan masana’antar suka yi zargin cewa ana musu bi-ta-da-kulli ne saboda bambancin siyasa.

Wasan sada zumunci tsakanin 13×13 da YBN

Domin kwantar da hankalin mutane, darakta Aminu S. Bono ya ce za su hada wasan kwallon kafa na sada zumunci tsakacinsu.

A cewarsa, “In sha Allah domin karfafa zumunci da dinke Kannywood za mu buga wasan kwallon kafa tsakanin YBN da 13×13.

Sannan ya kara da cewa, Nan gaba kadan za mu sanar da lokaci da wajen da za a buga wasan; Abu daya ne kuma ba za mu bari ya zama biyu ba in sha Allah.”

Akwai bambancin tsakanin YBN da 13×13-Naziru Dan Hajiya

Aminiya ta nemi jin ta bakin daya daga manyan masu shirya fina-finai a masana’antar, Naziru Auwal wanda aka fi sani da Dan Hajiya, inda ya ce akwai bambacin tsakanin tafiyar guda biyu.

“Kamar yadda suka ce, ita 13×13 ba ta siyasa ba ce, YBN kuma kungiya ce ta tallata dan takara.”

A game da abin da ke jawo rikici, sai ya ce, “Wasu a ciki suna amfani da kungiyar don jawo sabaninsu da wasu na kansu cikin tafiyar. Amma ai manufofin ba daya ba ne.”

A karshe Naziru ya shawarci bangarorin guda biyu da su hada kai, inda ya ce bai kamata abu kalilan ya shiga tsakaninsu ba.