✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yoyon fitsari: Za a yi wa mata 150 aiki kyauta da tallafi a Kano

Mata 150 masu lalurar yoyon fitsari a Jihar Kano za su ci gajiar aikin tiyata kyauta da kuma tallafin sana'o'in dogaro da kai.

Mata 150 masu lalurar yoyon fitsari a Jihar Kano za su ci gajiar aikin tiyata kyauta da kuma tallafin sana’o’in dogaro da kai.

Daga cikinsu, an zabo mata 50 masu fama da yoyon fitsari domin yi musu tiyata kyauta a Asibitin Kwararuu na Murtala Muhammad da ke Kano.

Karin wasu 100 masu lalurar ta yoyon fitsari da kuma za su samu tallafin dogaro da kai, kasnacewar a halin yanzu suna samun saki bayan an yi musu aiki.

Matan dai za su gajiyar wannan aiki da tallafi ne a karkashiin shirin taimakon al’umma a bankin First Bank a jihar Kano.

Da yake kaddamar da shirin, Babban Daraktan Hulda da Gwamnati na First Bank, Abdullahi Ibrahim, ya ce bankinsu ya dauki nauyin aikin ne tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano.

A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda Kwamishinar Harkokinn Mata da Walwalar Jama’a ta jihar, Zahrau Muhammad Umar, ta wakilta, ya jinjina wa bankin a bisa kokarin.

Ganduje ya kuma taya murna ga masu fama da lalurar da aka yi wa aikin da a halin yanzu suke kara samun sauki.