✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunkurin dage zabe ya sha kasa * Majalisar kasa ta ki yarda * Hukumar Zabe ta ce ta shirya

Yunkurin dage babban zaben kasar nan da za a gudanar a makon gobe ya sha kasa bayan da Majalisar kasa ta yi fatali da hakan,…

Yunkurin dage babban zaben kasar nan da za a gudanar a makon gobe ya sha kasa bayan da Majalisar kasa ta yi fatali da hakan, kuma wakilan majalisar suka tsaya kai da fata sai a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.

Taron wanda Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kira cikin gaggawa da aka gudanar a jiya Alhamis, bayan an shafe awa takwas ana tattaunawa wakilan majalisar sun yi fatali da yunkurin dage zaben. Sai dai sun ce ana iya dage zaben a jihohin da suke cikin hadari, kamar jihohin da Boko Haram suke kai hare-hare.
Dukkan tsofaffin shugabanninn kasa da suka hada da Alhaji Shehu Shagari da Janar Yakubu Gowon da Janar Muhammadu Buhari da Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar da shugaban gwamnatin riko Cif Ernest Shonekan, duk sun hallara, baya ga Cif Olusegun Obasanjo da bai halarta ba.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Dabid Mark da takwaransa na wakilai, Alhaji Aminu Tambuwal da tsohon Babban Jojin Najeriya Mai shari’a dahiru Musdafa da takwaransa Alfa Belgore da kuma gwamnoni 30 da suka fito daga jam’iyyun PDP da APC.
Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha wanda ya yi bayani ga manema labarai na fadar Shugaban kasa bayan tashi daga taron majalisar da Shugaba Goodluck Jonathan ya jagoranta.
Ya ce Shugaban Hukumar Zabe ta kasa ya ba majalisar tabbacin cewa hukumarsa ta gama shiryawa don gudanar da zaben fiye da kintsin da ta yi a zaben shekarar 2011.
Cif Okorocha ya ce hafsoshin tsaro da suka halarci taron sun nuna damuwa kan “wasu kananan hukumomi da suke fuskantar matsalolin tsaro.”
Ya ce: “Majalisar kasa ta shawarci INEC ta je ta sauke nauyin da ke kanta wato gudanar da zabe. Wannan shi ne abin da muka cimma matsaya. Lokaci ne na kalubale, kuma INEC ta sha nanatawa cewa ta kintsa, to amma sai hafsoshin tsaro suka rika nuna damuwa kan wasu kananan hukumomi, majalisar ta umarci INEC ta je ta yi aikinta wanda shi ne gudanar da zabe.”
Okorocha ya ce ba a yanke shawara kan sauya ranar zabe ko dage zabe ba ko kadan. Majalisar dai ta nemi INEC ta sauke nauyin da ke kanta.
Ya ce ba su tattauna wani batu kan rade-radin da ake yadawa cewa Farfesa Jega ya yi murabus ba. Kuma ya ce babu batun yin amfani da katin wucin-gadi tunda an riga an bayar da sababbi, kuma Farfesa Jega ya ba su tabbacin za a kammala bayar da sauran katin zabe na dindindin zuwa ranar Lahadi mai zuwa.
Ya ce ba lallai ne ra’ayin su ’yan APC ya zo daidai da na PDP ba, to amma tsarin mulki ne yake jagoranta wajen warware duk sabanin da aka samu. Ya ce, APC tana da yakinin zaben Shugaban kasa zai gudana a ranar 14 ga Fabrairu kamar yadda aka tsara.
Gwamnan Jihar Ondo Olusegun Mimiko, ya ce taron ya mayar da hankali ne kan batun zabe mai zuwa, kuma Jega ya yi wa majalisar bayani kan kintsin hukumar inda aka ba shi wasu shawarwari kan kintsin hukumar game da zaben.
Sai dai da aka tambaye shi ko an dage ranar zabe, sai ya ce ba shi ne INEC ba. An dai shawarci INEC kuma za ku ji daga Hukumar INEC din.
Sai dai wata majiya a wajen taron ta shaida wa wakilinmu cewa Jega ya shaida wa majalisar cewa wajibi ne a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.
Majiyar ta ce Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro, Sambo Dasuki, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta bayar da tabbacin tsaro ba a jihohi hudu na Arewa maso Gabas da suka hada da Yobe da Adamawa da Borno da Gombe.
A ranar Alhamis din makon jiya ne wata kafar labarai ta fallasa wani shiri da ta ce fadar Shugaban kasa da Jam’iyyar PDP na yi don shirya zanga-zanga a fadin kasar nan saboda a tilasta wa Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta dage zaben.
Mashawarcin Shugaban kasa, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya ne ya fara kiran a dage zaben a wajen wani taro a Landan kwanakin baya da sunan a ba Hukumar INEC karin lokaci don ta rarraba katin zabe na dindindin.
A ranar Litinin wasu matasa 100 sun gudanar da zanga-zanga a harabar Hedkwatar Hukumar INEC, suna neman hukumar ta dage zaben. Matasan suna neman hukumar ta jinkirta gudanar da zaben ne, wai saboda wahalar rarraba kati zabe na dindindin da ake fuskanta.
Shi dai wannan kira ya samu kausasan soke-soke, inda babbar jam’iyyar adawa ta APC ta zargi Sambo Dasuki da yin kiran domin ba wa dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Dokta Goodluck Jonathan damar kara dabarun yakin neman zabensa.
Tun daga lokacin da Sambo Dasuki ya yi wannan kira kungiyoyi da daidakun mutane suka fara kiran a dage zaben.
Masu zanga-zangar dai sun ce kashi 40 cikin 100 ne kawai suka karbi katin zabe na dindindin don shiga zaben na ranar 14 ga Fabrariru. Sun kuma ce Hukumar INEC tana bukatar ma’aikatan wuci-gadi dubu 960, amma har zuwa lokacin da sukie zanga-zangar ba dauki ma’aikatan ba, inda suka ce idan aka ce za a yi zaben yadda aka tsara miliyoyin ’yan Najeriya ba za su iya kada kuri’arsu ba.
Jam’iyyar APC ta hannun kakakinta Lai Mohammed ta fitar da sanarwa a shekaranjiya Laraba, tana cewa wata talla a jarida ta nuna a fili bukatar dage zaben tana fitowa ne daga PDP da fadar Shugaban kasa.
“Ba a samu wata manuniya a fili cewa PDP da fadar Shugaban kasa suna da hannu a shiri dage zabe ba, sai a tallar da aka buga a wata jarida ranar Laraba wadda a fili take kira a dage zaben,” inji APC.
“Wannan talla wadda ke dauke da hoton Shugaban kasa da tambarin PDP na nufin su ne za su ci gajiyar dage zaben da suke nema- kuma hakan ba shakka ya nuna jam’iyya mai mulki da fadar Shugaban kasa ba su da gaskiya, kuma suna yaudara da gangan kuma suna matukar tsoron a gudanar da zabe,” inji Mohammed.
Batun neman a dage zaben ya kara zafafa bayan da wasu jam’iyyun siyasa 16 da wasu ’yan takarar Shugaban kasa hudu suka fito suna neman a dage zaben.
Mai magana da yawunsu kuma dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar UDP, Godson Okoye ya fadi a ranar Talata, cewa jam’iyyun da suke so a dage zaben sun hada da UDP da CPP da PPN da AA da PDC da LP da UPN da kuma AD da DPP da NNPP da ID.
’Yan takarar Shugaban kasa da suka nemi a dage zaben kuma sun hada da Sam Ekeh na CPP da Anifowose Kelani na AA da Ganiyu Galadima na ACPN.
Jam’iyyun sun ce dage zaben ba zai saba wa sashi na 25 da 26 na dokar zabe ba, maimakon haka zai ba INEC cikakken lokaci ta rarraba katin zaben na dindindin.
Jam’iyyun sun ce ba za su shiga zaben ba, muddin INEC ta ki sauraren kiransu na a dage zaben. Kuma sun soki Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry kan ganawa da ’yan takarar Shugaban kasa na jam’iyyun PDP da APC, Shugaba Jonathan da Janar Buhari a lokacin ziyararsa a kasar nan.
Sai dai dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar UPP, Mista Chekwas Okorie ya yi watsi da kiraye-kirayen a dage daben, inda ya ce tunda INEC ta ce an raba kimanin kashi 80 na katin zabe na dindindin babu bukatar a dage zaben.
Tun kafin halartar taron Majalisar kasa tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce bai kamata mutane su rika tunanin a dage zaben ba.
Janar Babangida ya shaida wa BBC cewa tunda hukumar zabe ta ce ta shirya, ya kamata a ba ta dama ta gudanar da aikinta na tabbatar da zabe cikin gaskiya da adalci.
Babangida ya ce “Hukumar zabe ta tabbatar mana ta shirya domin gudanar da wannan zabe don haka babu batun dage zabe.”
Sai dai ya ce, “Ina kira ga mutane su san cewa zabe zai zo ya wuce domin haka su zauna lafiya kada su tayar da hankali.”
Wata kungiya a karkashin tsohon ministan labarai a Jamhuriya ta daya kuma ubangidan siyasar Shugaba Jonathan Cif Edwin Clark da suka kira Majalisar Al’ummar Kudancin Najeriya sun ma bukaci Shugaban Hukumar INEC Farfesa Attahiru Jega ne ya yi murabus saboda ya nace kan zai gudanar da zaben a mako mai zuwa.
kungiyar wadda ta gudanar da taron manema labarai a Abuja a jiya Alhamis, inda wasu ’yan siyasa daga Kudu da suka hada da tsohon Ministan Labarai Walter Ofonagoro da tsohon Gwamnan Jihar Anambra Dokta Chuwuemeka Ezeife da wani tsohon kwamishina a Jihar Bayelsa, Cif Whisky Ayakeme da Dokta Cairo Ojugboh da kuma Sanata Femi Okunronmu wadanda dukkansu cikakkun magoya bayan Shugaba Jonathan ne suka halarta.
Mahalarta taron sun yi barazanar cewa mutane Kudu za su kaurace wa zaben na makon gobe muddin Hukumar INEC ta yanke shawarar gudanar da zaben.
Kwamitin yakin neman zaben Shugaban kasa na Jam’iyyar APC ya ce rashin dage zaben ya magance matsalar da za a fuskanta game da zaben.
Kakakin kwamitin Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa jim kadan da samun bayanin cewa Majalisar kasa ta yi fatali da yunkurin dage zaben.