✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunkurin hana ni tikitin APC ya dugunzuma ni —Tinubu

Dole ce ta sanya na koma na dukufa wajen kai wa Allah kukana da addu’o’i.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce yunkurin hana shi samun tikitin jam’iyyar ya tayar masa da hankali matuka.

A cewarsa, ya fito ya yi ta maganganu a lokacin da ya ji a jikinsa cewa wasu mutane sun yi masa taron dangi don hana shi cimma muradinsa a sakamakon neman tikitin tsayawa takarar shugabancin kasar da yake yi a jam’iyyar APC.

Tinubu ya bayyana gumurzunsa da irin halin da ya shiga kafin samun tikitin na APC yayin da ya ziyarci Fadar Oba na Legas, Rilwan Akiolu a ranar Lahadi.

Dan takarar shugaban kasar ya ce har sai da aka kai lokacin da ya ji komai ya gundure shi, lamarin da ya sanya ya koma ya dukufa wajen kai wa Allah kukansa da addu’o’i.

Da yake ci gaba da jawabi, Tinubu ya ce babu wani dan asalin Jihar Legas da ya taba samun damar zama shugaban Najeriya, duk kuwa da gudummawar da jihar ta bayar wajen hadin kan kasar.

Ya ce babban mukami da wani dan Jihar Legas ya taba samu a Gwamnatin Tarayya shi ne Babban Lauyan Kasa, wanda wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sanya shi yanke shawarar neman kujerar Shugaban Kasa.

Tinubu wanda tsohon Gwamnan Jihar Legas ne ya ce babban kalubalen da ke gabansa a yanzu na gani hakarsa ta cimma ruwa shi ne tabbatar da al’umma sun mallaki katin zabe sannan kuma sun fita sun jefa kuri’a a lokacin zaben.

Aminiya ta ruwaito cewa Tinubu ya samu galaba a kan a kan ’yan takara 13 da suka fito neman jam’iyyar APC ta tsaida su takarar shugabancin Najeriya a babban taron jam’iyyar da ya gudana a Abuja.

A makonnin bayan nan dai Tinubu ya mamaye kafofin yada labaran Najeriya gabanin zaben fid da dan takarar Shugaban Kasa, musamman a lokacin da ya fito yana goranta wa Shugaba Muhammadu Buhari da cewa ba don shi ba da bai samu kujerar da yake kai a yanzu ba.

Haka kuma dai zancen Tinubu ya ci gaba da gudana a harsunan jama’a kusan a kowane kwararo da sako na kasar nan da ma ketare kan cewa shi ne ya fito da Shugaba Buhari daga murabus din da ya yi a siyasa.

Kazalika, Tinubu ya kuma yi ikirarin cewa shi ya dora Dapo Abiodun a kan kujerar gwamnan Jihar Ogun, kana ya zabi Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai zama Mataimakin Shugaban Kasa.