Yunwa ta kara tsanani a kasashen Larabawa —MDD | Aminiya

Yunwa ta kara tsanani a kasashen Larabawa —MDD

    Sagir Kano Saleh

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum daya a cikin kowane mutum uku a kasashen Larabawa na fama da yunwa a halin yanzu.

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum miliyan 69 ne suka yi fama da rashin lafiyayyen abinci a fadin yankin Larabawa a shekarar da ta gabata.

Rahoton da hukumar ta fitar ranar Alhamis ya ce, “An samu karuwar masu fama da yunwar ne a kowane rukuni na al’umma, a kasashen da ake fama da rikice-rikice da ma wadanda da ba a yi.

“Bugu da kari, mutum miliyan 141 sun yi fama da rashin abinci a 2020 – wanda ke nufin an samu karin mutum miliyan 10 idan aka kwatanta da 2019,” a cewar rahoton.

Ya kara da cewa bullar annobar COVID-19 ta kara wa lamarin tsanani da mutum miliyan 4.8 idan aka kwatanta da alkaluman 2019.

Rahoton ya bayyana cewa matsalar ya fi kamari a kasashen Somaliya da Yemen da ke fama da yake-yake, inda kashi 60 na al’ummar Somaliya da kashi 40 na mutanen Yemen ke cikin wannan yanayi.