✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunwa ta sa ’yan bindiga fara shirin satar amfanin gona – Masari

Ya alakanta hakan da yadda suke ci gaba da matsowa zuwa garuruwa.

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya ce ’yan bindiga a Jihar za su iya satar kayan amfanin gonar da manoma suka sami damar nomawa a Jihar.

Ya alakanta hakan da yadda suke ci gaba da matsowa zuwa garuruwan kusa da dazuka sanadiyar hare-haren da ake kai musu ta sama da kasa.

A cewarsa, tsananin yunwar da suke fuskanta ya tilasta musu fitowa domin shiga cikin jama’a da nufin neman abinci ko neman mafaka.

Masari ya furta hakan ne a Gidan Gwamnatin Jihar ranar Talata lokacin da ya karbi bakuncin Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Muhammad.

Dagan an sai Gwamnan ya ankarar da jami’an tsaro kan su dauki matakin gaggawa a kan lamarin.

A kwanan nan ne dai NCC ta umarci kamfanonin sadarwa da su datse dukkan hanyoyin sadarwar a Jihar Zamfara da kuma wasu Kananan Hukumomi guda 13 na Jihar Katsina a matsayin irin matakan da ake dauka don magance matsalar ayyukan ’yan bindiga a yankin.

Kazalika, sojoji kuma na ci gaba da luguden wuta ta sama da ta kasa ga ’yan bindigar da suka kafa sansanoni a dazukan yankunan.