✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunwa za ta tagayyara mutanen Yemen matukar babu agaji —MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a mayar sa hankali kan halin da kasar Yemen ke ciki.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce bai kamata a manta da halin kuncin rayuwa da matsananciyar yunwar da al’ummar kasar Yemen ke ciki ba saboda yakin Rasha da Ukraine.

Majalisar ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar bala’in yunwa a kasar idan ba a ba wa mutanen kasar gudummawar da ta dace ba.

Ta yi kiran ne a taron da ta shirya kan cika alkawarin tallafa wa gidauniyar ci gaba da baiwa Yemen agaji a ranar Laraba.

Tun da jimawa, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana Yemen, wadda yaki ya daidaita, a matsayin kasar da aka fi fuskantar bala’in tagayyarar mutane a duniya; A yanzu kuma karancin kudaden tallafi sun sanya yanayin ya kara ta’azzara a kasar.

A wani jawabi da ya gabatar, Shugaban Hukumar Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths, ya ce a bana kadai ana bukatar tallafin kusan Dala biliyan hudu da rabi domin taimaka wa mutane fiye da miliyan 17 a kasar ta Yemen.

Sai dai a yayin da kudaden tallafin ke karewa tun daga karshen shekarar da ta gabata, hakan ya tilasta wa hukumomin agaji ragewa ko dakatar da ayyukan rabon tallafin  kayan abinci da kiwon lafiya a kasar.

Wata kididdigar majalisar ta nuna cewa a cikin mutum kusan miliyan 32, kimanin mutum miliyan 23 da rabi na bukatar agajin jinkai, miliyan 12 da dubu 900 kuma na cikin tsananin bukatar agajin gaggawa.

Kasar Yemen ta fada cikin kazamin yaki ne a shekarar 2014, inda ake fafatawa da ’yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan kasar Iran da gwamnatin kasar da kasashen duniya suka amince da ita, wadda kuma take samun goyon bayan sojojin kawancen kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta.

Yakin ya salwantar da rayukan dubban mutane, sannan ya jefa kasar cikin wani mummunan yanayi da matsananciyar yunwa.