✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a ba manoman zogale 2,500 tallafi a Katsina

Nan ba da jimawa ba manoman zogale a Jihar Katsina za su samu tallafi na musamman domin karfafa musu wajen bunkasa harkokinsu a jihar.

Nan ba da jimawa ba manoman zogale a Jihar Katsina za su samu tallafi na musamman domin karfafa musu wajen bunkasa harkokinsu a jihar.

Kawo yanzu, shiri ya kankama tsakanin gwamnatin jihar da Kungiyar Manoma da ‘Yan Kasuwar Zogale ta Kasa (NAMFAPMAN), don tallafa wa manoman zogale 2,500 a fadin jihar.

Mataimakin Shugaban Kungiyar na kasa, Malam Rabe Hashimu ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labara na Najeriya (NAN) hakan ranar Litinin a Katsina.

Hashim ya ce, gwamnatin jihar ta bai wa manoman tabbacinta na shirya daukar nauyin ba da horo na musamman kan sabbin dabarun noman zogale ga wadanda za su ci gajiyar shirin.

Don cim ma wannan kudiri kuwa, Hashim ya ce gwamnati ta ware filin noma kadada uku a kowace Karamar Hukuma daga Kananan Hukumomi 34 da jihar ke da su wanda za a yi amfani da su wajen shirin.

Zogale na daga cikin tsirran da aka bai wa fifiko wajen noman su a wannan zamani saboda dimbin alfanun da yake tattare da su.

Noman zogale ka iya zama hanyar samun kudin shiga da samar da aikin yi ga duk jihar da ta rike shi hannu biyu-biyu, saboda bukatar zogale ba ta tsaya a gida Najeriya kadai ba, har da kasashen ketare.

(NAN)