Daily Trust Aminiya - Za a bai wa mahaifiyar Rashidi tallafin N10,000 duk wata
Subscribe

Alhaja Sikiratu Yekini mahaifiyar marigayi Rashidi Yekini

Za a bai wa mahaifiyar Rashidi tallafin N10,000 duk wata

Ministan Wasanni Sunday Dare ya ce gwamnatin tarayya za ta fara bayar da tallafin kudi a ko wanne wata ga mahaifiyar marigayi Rashidi Yekini.

Sunday Dare ya fadi haka ne ta bakin wakilinsa, Olaitan Shittu, ranar Laraba lokacin da yake mika kayan abincin azumi da kudi N50,000 ga Alhaja Sikiratu Yekini a gidanta dake kauyen Ijagbo a kusa da garin Offa na Jihar Kwara.

Da yake mika kayan a madadin ministan, Mista Shittu ya ce gwamnati za ta rinka bayar da wannan tallafin duk wata ga tsohuwar har tsawon ranta.

A baya ma dai ministan ya saba aika wa tsohuwar da tallafi daga aljihunsa.

Da take karbar wannan kaya Alhaja Sikiratu Yekini ta nuna matukar farin cikin ta ga ministan.

“Na fada cikin kuncin rayuwa tun lokacin da dana ya rasu domin ba na samun taimako daga mutane kuma su ma ’yan uwansa ba sa taimaka mani kamar yadda ya dace; shi ne ya sa aka bar ni ina fafutuka ni kadai a kowace rana”, inji alhaji Sikiratu.

Ta ci gaba da cewa an jingine ta waje daya an manta da ita wanda ya kai ta ga fadawa rashin lafiyar da ya kwantar da ita a asibiti.

Alhaja Sikiratu Yekini, mahaifiyar marigayi Rashidi Yekini (a dama) a lokacin da take karbar tallafin kayan abincin azumi daga wakilin Ministan Wasanni Sunday Dare

Ta ce tana matukar bukatar taimakon mutane domin kula da rayuwar ta.

Marigayi Rashidi Yekini, wanda ke cika shekara takwa da rasuwa, ya taka leda wa tawagar Super Eagles a ciki da wajen Najeriya.

More Stories