✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a binciki dan sandan da ya ‘kada kuri’a’ a zaben APC na Kano

Rundunar ta bayyana abin da jami’in ya yi a matsayin wanda ya saba da ka’idar aikinsa.

Rundunar ’Yan Sanda ta umarci a binciki jami’in dan sandan da hotunansa suka karade shafukan sada zumunta inda aka ganshi yana kada kuri’a a zaben shugabannin APC a Jihar Kano na ranar Asabar.

A cikin hoton dai, an hangi jami’in dan sandan a kusa da sabon zababben Shugaban APC tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje, wato Abdullahi Abbas, yana jefa kuri’arsa a akwatin zabe.

To sai dai a cikin wata sanarwa da Shiyya ta Daya ta Rundunar ’Yan Sandan da ke Kano ta fitar ta bakin kakakinta, Abubakar Zayyanu, rundunar ta ce Mataimakin Babban Sufeto mai kula da shiyyar, AIG Abubakar Sadiq Bello ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

A cewar sanarwar, AIG din ya bayyana abin da jami’in ya yi a matsayin wanda ya saba da ka’idar aikinsa.

Aminiya ta gano cewa jami’in dan sandan mai suna Bashir Mohammed yana aiki ne a Gidan Gwamnatin Kano kuma an wakilta shi a matsayin dogarin Abdullahi Abbas.

Sanarwar ta ce, “Saboda wannan abin da ya aikata, AIG ya ba da umarnin a fadada bincike a kai.

“Muddin aka same shi da aikata laifin, to tabbas za a dauki matakin da ya dace a kansa.”

Dagan an sai rundunar ta ba da tabbacin cewa za ta sanar jama’a dukkan wani ci gaba da aka samu a kan batun a nan gaba.