✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a biya ma’aikatan da suka rasu N9.2bn

Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da Dokar Kudi ta 2022

Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan Naira biliyan 9.2 a matasayin kudin inshorar rayuwar ma’aikatan gwamnati da suka rasu na shekarar 2022 da 2023.

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta yi hakan ne a zaman da ta amince da Dokar Kudi ta 2022 wadda aka samar musamman don tallafa wa aiwtar da kasafin 2023.

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce, “Inshorar ta shafi daukacin hukumomin gwamnati da na tsaro.

“Majalisar ta amince da ware Naira biliyan  9.24 don amfanin inshorar daga 2022 zuwa 2023.”

Ta kara da cewa inshorar, wadda Shugabar Ma’aikatan Gwamnati Tarayya ta gabatar da daftarinta na 2022 zuwa 2023, “Za ta fara aiki ne daga ranar da aka biya.”

A jawabinta bayan zaman da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya jagoranta a Fadar Shugaban Kasa, ministar ta ce, “Bisa tsarin dokar Najeriya, kashi 30 cikin 100 na albashin shekara duk ma’aikacin gwamnatin da ya mutu zai samu.

“Sannan kamfanin inshorar da ma’aikacin ya yi rajista da shi ne zai biya kudin.