✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a biya masu sharar kwata albashin N20,000

Gwamnatin Tarayya na shirin biyan albashin N20,000 ga mutanen da za ta dauka aikin shara da gyaran magudanan ruwa a fadin Najeriya. Karamin Ministan Kwadago…

Gwamnatin Tarayya na shirin biyan albashin N20,000 ga mutanen da za ta dauka aikin shara da gyaran magudanan ruwa a fadin Najeriya.

Karamin Ministan Kwadago da Daukar Aiki Festus Keyamo ya ce an bullo da shirin Ayyukan Al’umma na Muwamman (SPW) ne domin mazauna yankuna su amfana.

A cewarsa, shirin zai dauki matasa 1,000 a kowacce daga kananan hukumomi 774 na kasar nan; shi ne mafi girma da gwamnati ta taba yi na samar da ayyuka kai tsaye.

Gwamnati ta ware naira biliyan 42.6 domin biyan matasan albashinsu da zarar sun fara aikin na tsawon wata uku daga watan Oktoba mai zuwa, inji shi.

Ayyukan da matasan za su yi sun hada da sharar tituna da gine-ginen gwamnati da kuma bayar da hannu a kan tituna.

Akwai kuma gyara da yasan kwatoci da magudanai da madatsan ruwan yankunan karkara da na noman rani.

Za kuma su rika aiki a gandun rainon shuke-shuke a jihohin Borno, Katsina da Jigawa, na nufin takaita kwararowar hamada.

Keyamo ya ce nan gaba za a bude shafin daukar masu sha’awar aikin kafin daga bisani a fitar da sunayen wadanda suka yi nasara.

Kwamitin daukar ma’aikatan zai hada da zababbun ‘yan siyasa hana masu neman yin kaka-gida a daukar aikin.

A baya Keyamo ya yi barazar sauka daga mukaminsa muddin ‘yan siyasa suka yi kokarin hana shirin isa ga talakawa.

A cewarsa kashi 10 na gurabun aikin ne kacal za a ba sanatoci da ‘yan majalisar wakilai da gwamnoni da ministoci.

Shugaba Buhari ya fara kirkiro da shirin daukar matasa 1,000 aikin wata uku a kowace karamar hukuma ne da zuman samar da ayyuka.