✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a biya ’yan fansho karin kudi a watan Mayu

Za a biya su bashin hakkokinsu na shekara biyu tun daga 2019.

Shugaba Buhari ya ba da umarnin biyan ’yan fanshon Gwamnatin Tarayya karin kudadensu tun daga shekarar 2019.

Hukumar Kula da Fansho ta Kasa (PTAD), ta ce za a biya ’yan fanso bashin karin da aka yi musu ne tun daga watan Afrilun 2019.

“Da wannan izinin, PTAD ta samu karfin yin kari ga dukkannin hakkokin ’yan fansho,” inji  Shugabar Hukumar, Chioma Ejikeme.

Ta ce daga watan Mayun 2021 za a fara biyan su bashin kudaden, a kuma ci gaba da biyan hakkokin ’yan fanshon bisa sabon tsarin albashin ma’aikata na shekarar 2019.

Shugabar ta jaddada cewa PTAD ba za ta bukaci ko sisi daga hannun ’yan fansho a matsayin na goro ba, kafin a biya su hakkokinsu.

Don haka ta shawarce su da su yi hattara kar su fada hannun ’yan damfara da masu ci da gumin wasu.