✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah za ta tilasta masu son aure a Kano shiga makarantar koyon zamantakewa

Hukumar ta ce nan gaba shiga makarantar zai zama tilas ga masu bukatar yin aure.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta bude makarantar koyon zamantakewar aure a Jihar, a watan Nuwamban 2021.

Babban Kwamandan hukumar, Malam Muhammad Haruna Ibn Sina ne, ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan rediyon Freedom a Kano.

Ibn Sina ya ce, a matakin farko zabi ne ga wanda ke da sha’awar shiga, amma a nan gaba za su yi kokarin ganin an mayar da shi doka ga duk mai son yin aure a Kano.

“Kaso 75 daga cikin korafin da mu ke karba kan matsalolin aure ne, wannan ne ya sanya muka samar da makarantar don ba da horo.

“Matsalar yawaitar mutuwar aure a kullum karuwa take musamman a Kano, don haka makarantar za ta samar da hanyoyin dabarun koyar da ilimin zamantakewar aure,” cewar Ibn Sina.

Kazalika, kwamandan ya kara da cewa za su shigar da kudiri gaban majalisar dokokin Jihar don tilasta wa ma’aurata shiga makarantar.

Ibn Sina, ya kuma kara da cewa horaswar ba iya mata za ta tsaya ba, har da maza za a basu damar shiga don samun daidaito da raguwar matsalolin.

Matsalar aure a Jihar Kano na ci gaba da zama babbar kalubale musamman kan yadda Hisbah ke fama wajen warware su.