✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a dauki nauyin karatun gurguwar da ke rarrafen zuwa makaranta har jami’a

gurguwa mai yin rarrafen akalla kilomita daya a kullum domin zuwa makaranta da ya karade gari a kwanakin baya

Biyo bayan rahoton wata yarinya gurguwa mai yin rarrafen akalla kilomita daya a kullum domin zuwa makaranta da ya karade gari a kwanakin baya, a yanzu haka dai an gwangwaje ta da sha tara ta arziki.

A kwanakin baya ne Aminiya ta rawaito yadda yarinyar, mai suna Fatima Shu’aibu wacce mazauniyar kauyen Dan Shayi ce a Karamar Hukumar Rimin Gado ta jihar Kano ta ke rarrafen zuwa makaranta a kullum sakamakon rashin keken guragu.

Hakan ya janyo hankalin daidaikun mutane, hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu wajen tallafa mata.

Daga cikin wadanda suka tallafa mata sun hada da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), Cibiyar Fasahar Sadarwa ta Zamani ta Penlight, da dai sauransu.

Kayan tallafin da ta samu sun hada da kudade, littattafai, jakunkuna, sutturu, kekunan guragu guda takwas da kuma daukar nauyin karatun ta har zuwa matakin jami’a.

Kazalika, cibiyar Penlight karkashin jagorancin shugabanta, kuma mawallafin jaridar intanet ta Daily Nigerian Ja’afar Ja’afar da hadin gwiwar takwararta Arewa Agenda sun kafa wata gidauniya domin ci gaba da tallafawa rayuwarta.

Ja’afar ya kuma ce yanzu haka suna shirin kai ta zuwa asibiti domin a duba yuwuwar tallafa mata ko za ta iya tafiya da sanda.

“Da sama da N800,000 da muka tara yanzu haka, za mu ware wani kaso mai tsoka daga ciki wajen kula da bukatun ta na yau da kullum na bangaren abinci, lafiya, suttura da kuma muhalli.

“Muna kuma duba yuwuwar tallafawa kakarta ta hanyar samar mata da sana’ar da za ta rika kawo mata kudaden shiga don ta iya ci gaba da kula da ita.

“Za mu dauki malami na musamman wanda za mu rika biya domin ya rika yi mata darasi, tare kuma da biyan kudin makarantar ta har zuwa matakin jami’a,” inji Ja’afar.

Sauran wadanda suka ba da tallafin sun hada da Cibiyar tallafawa masu bukata ta musamman ta Beautiful Gates, Kabiru Alhaji Haruna Gimba na Kamfanin Sarrafa Karafa na Ajaokuta, Hadiza Umar ya hukumar NITDA, shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafe ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado, Ibrahim Sunusi Ismail, Modu Kachalla Bole da kuma Jibril Mahmud.

Sauran sune Hajiya Madina da kawayenta, Garba Mohammad Sadiq, Abdullahi Aminu Mudi, Moses Ebe, Mohammad Aminu Mohammad da dai sauransu.