✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a daure ta shekara 5 saboda kai wa saurayinta kwaya gidan yari

Ana dai zarginta da yunkurin shigar wa da kwayoyin gidan yarin Jos

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jos, Jihar Filato ta yanke wa wata budurwa hukuncin daurin shekara biyar saboda yunkurin shigar wa da saurayinta da ke tsare a gidan yari da kwayoyi.

Ana zargin budurwar mai kimanin shekaru 22 da kunshe kwayoyin a cikin wani mazubi sannan ta yi yunkurin shigar wa saurayin nata da su gidan yarin birnin Jos, kafin dubunta ta cika ma’aikatan gidan su kama ta.

Kwayoyin dai sun hada da tabar wiwi wacce nauyinta ya kai kusan Giram 700, da kuma kwayar Diazepam mai nauyin Giram 43.2.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta kama budurwar dumu-dumu da laifin.

Bayan gurfanar da ita a gaban kotun da ke karkashin Mai Shari’a Musa Kurya, wacce ake zargin ta amsa aikata laifin da ake zarginta da aikatawa.

Da yake yanke hukuncin, alkalin ya ce hukuncin zai zama izina ga wadanda suke da irin wannan dabi’ar.

Tun da farko dai lauya mai shigar da kara, Uche Chukwu, ya shaida wa kotun cewa laifin da ake zargin Celine da aikatawa ya saba wa tanade-tanaden Sashe na 19 na Dokar Hukumar NDLEA na shekara ta 2004 wanda aka yi wa kwaskwarima.

Sai dai lauyan da ke kare wacce ake zargi, Joshua Akubo, ya roki kotun da ta sassauta mata, la’akari da karancin shekarunta.