✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a dawo da karbar harajin motoci a manyan titunan Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta amince da sake dawo da karbar haraji daga motoci a manyan titunan da ke fadin kasar. Hakan ya biyo amincewar da taron…

Gwamnatin Tarayya ta amince da sake dawo da karbar haraji daga motoci a manyan titunan da ke fadin kasar.

Hakan ya biyo amincewar da taron Majalisar Zartarwa ta tarayya ya yi a zamansa na ranar Laraba.

Sai dai harajin ba zai shafi motocin gwamnati ko sojoji da ma’aikatu da bubura da kekuna ba.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola da ke ba da wannan tabbacin a jiya Laraba a Abuja.

A cewarsa, an dau matakin ne domin kara hanyoyin samun kudaden shiga.

Sannan ya ce dama tun a zamanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo a 2003 aka kirkiro wannan haraji, amma aka watsar don haka yanzu za a dawo da tsarin

Ministan ya ce kananan motoci za su ke biyan naira 200, manyan motoci kuma naira 500.