✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a dawo wa Donald Trump shafukansa na Facebook da Instagram

Kamfanin Meta mamallakin shafukan Facebook da Instagram ya ce zai bai wa tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, damar dawo da shafukansa na Facebook da Instagram,…

Kamfanin Meta mamallakin shafukan Facebook da Instagram ya ce zai bai wa tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, damar dawo da shafukansa na Facebook da Instagram, da ya rufe shekaru biyu da suka gabata.

Cikin wata sanarwa da shugaban sashin hulda da jama’a na kamfanin, Nick Cleggya, ya fitar,  ya ce akwai sharudda da kamfanin ya sanya kafin yin hakan, don gudun maimaita abinda ya faru a baya.

A cewar sanarwar, “Za mu dawo da shafukan Trump da muka rufe a baya nan ba da jimawa ba, amma akwai dokoki da muka saka don tabbatar da bai kuma karya ka’idojinmu ba.

“Idan kuma ya saba su, duk doka daya da ya karya dakatarwar shekaru biyu ce,” in ji Clegg.

Sai dai ta shafin da Trump din ya bude mai suna Truth Social ya yi martanin cewa rashinsa a shafukan ya janyo wa kamfanin asarar bilyoyi ne, shi ya sa Metan ke kokarin dawo masa da shufukan nasa.

“Bai kamata tun farko a ce haka ta faru ga wani shugaban kasa da ke kan mulki ba ko ma kowanne mai amfani da shafukansu” in ji shi.

Facebook dai ya rufe shafin Trump ne bayan magoya bayansa sun yi kokarin dakatar da shaidar faduwa zaben da suka kara da Shugaban Kasar mai ci, Joe Biden, ta hanyar kutsawa ginin Majalisar Dokokin Kasar da ke birnin Washington.

Shi ma dai kamfanin Twitter karkashin sabon shugabansa, Elon Musk ya dawo wa da Trump shafinsa na can tun a watan Nuwamban 2022 jim kadan bayan abyyanana aniyarsa ta fitowa takarar shugaban kasar karo na uku, sai dai har yanzu bai rubuta komai a cikinsa ba.