✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a debi matasa 10,000 aikin gadin bututan mai a Kogi

Za a debi matasan ne don a dakile ayyukan masu fasa bututan mai a Jihar.

Kungiyar Yankuna Masu Arzikin Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (HOSTCON), reshen Jihar Kogi ta kammala shirin dibar matasa 10,000 aikin gadin bututan mai a Jihar.

Shugaban kingiyar a Jihar, Gabriel Ojoka, ne ya bayyana hakan a Lokoja ranar Litinin.

Yana bayanin ne lokacin da ya jagoranci wani ayari domin ziyarar neman hadin kai ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Idris Dabban.

Gabriel, wanda kuma shi ne shugaban HOSTCON na Arewacin Najeriya ya ce dibar matasan ya zama wajibi don a dakile ayyukan masu fasa bututan a Jihar.

Ya ce daukar matakin ya yi daidai da umarnin Gwamnatin Tarayya ga dukkan jihohi masu albarkatun mai na su samar da irin wannan tsari, inda ya ce tuni wasu jihohin ma suka kammala.

“Mun zo ne don neman hadin kan ’yan sanda don tabbatar da cewa dukkan abin da za mu yi yana kan ka’idar ayyukan tsaro.

“Saboda haka, a shirye muke mu ba ku dukkan bayanan abubuwan da muke yi a Jihar Kogi,” inji Gabriel.

Da yake mayar da martani, Kwamishinan ’Yan Sandan ya ba su tabbacin cewa a shirye rundunarsa take ta ba da dukkan hadin kan da ake bukata. (NAN)