✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara biyan daliban jami’a alawus din N75,000

Gwamnati na kokarin fara ba wa wadanda suka karanci fannin ilimi aiki kai-tsaye.

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan alawus din Naira 75,000 ga dalibai masu karatu a fannin ilimi a matakin digirin farko.

Dalibai masu karatu a fannin ilimi a matakin neman shaidar kwarewa malumta (NCE) kuma za a rika biyan su alawus din N50,000.

“Domin jawo mutane mafiya kaifin basira su karanci fannin ilimi, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a rika biyan alawus din N75,000 ga daliban da ke karatu a matakin digirin farko a fannin ilimi a kowane zangon karatu.

“Su kuma masu karatu a matakin neman shaidar kwarewar malunta (NCE) kuma za a rika biyan su alawus din N50,000 kowannensu, kamar takwarorinsu da ke matakin digirin farko a jami’o’in gwamnati,” kamar yadda Hadimin Shugaba Kasa kan Kafafen Sada Zumunta, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Da yake sanar da matakin, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya kara da cewa Majalisar Ilimi ta Tarayya za ta bullo da wani tsari ta yadda gwamnatocin jihohi da cibiyoyin ilimi za su rika ba wa daliban da suka karanci fannin ilimi aikin kai tsaye a makarantun firamare da zarar an yaye su daga jami’o’i da kwalejojin ilimi.

Ya bayyana cewa za a rika biyan daliban alawus din karatun ne a kowane zangon karatu, a yunkurin gwamnati na jan ra’ayin dalibai masu basira su rungumi fannin ilimi domin inganta bangaren a Najeriya.

A jawabinsa ga taron bikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2021 da ya gudana a Abuja ranar Talata, ministan ya bayyana cewa daliban da ke karatu a makrantun gwamnati ne za su amfana da wannan alawus.

Ya bayayna hakan ne ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Mista Sonny Echono, wanda ya wakilce shi a wurin taron wanda ya gudana a Dandalin Eagles Square da ke Abuja.