✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara biyan kudin tantance masu amfani Facebook da Instagram

Akwai masu sojan-gonar da ke yi damfarar mutane da sunan wani da bai ji ba bai gani ba.

Kamfanin Meta mai kafofin sadarwa Facebook da Instagram zai fara karbar kudi don tantance shafukan mutane.

Kamfanin Meta ya sanar da hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata.

Ya bayyana cewar zai kaddamar da wannan tsari ga mai bukatar tantance shafinsa ko dai na Facebook ko kuma na Instargram.

Sai dai tsarin zai bukaci biyan wasu ’yan kudade.

Shugaban Kamfanin, Mark Zuckerberg ya ce sun fito da wannan tsarin ne domin kaucewa masu amfani da hotunan ko sunayen wasu mutanen na daban suna cewa su ne.

Zuckerberg ya ce a wasu lokutan ana samun masu sojan-gonar da yi wa jama’a damfara da sunan wani da bai ji ba bai gani ba.

A kowace alamar ta tantancewar ta Meta za ta kai dalar Amurka 12 ko kuma 15 kwatankwacin naira dubu 5 ko kusan dubu 7 ga kowane shafi.

Mark Zuckerberg ya ce wannan sabon shirin zai fara aiki ne a wannan makon da muka shigo a kasashen Australiya da New Zealand kafin daga baya su isa wasu kasashen.