✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara biyan mata masu al’ada kudi a Spain

Spain za ta kasance kasa ta farko da ta fara biyan kudin a nahiyar Turai.

Gwamnatin kasar Spain ta amince da kudurin dokar bayar da hutu da kuma biyan kudin hutu ga mata a lokacin da suke jinin al’ada.

Majalisar zartarwar kasar ta amince da kudirin dokar wadda ita ce ta farko a kasashen Turai, ta yadda duk wata mace da kan fuskanci matsala lokacin al’adarta, za ta dauki kwanakin hutu yadda take so.

Kazalika, gwamnatin kasar ta Spain za ta biya ta ba tare da dora wa kamfanin da take aiki nauyin ba.

Sai dai likitoci ne kadai ke da hurumin tabbatar da irin wadannan matan da ke fuskantar matsaloli lokacin al’adarsu.

Bayan amincewar majalisar, yanzu za a gabatarwa majalisar dokoki kudirin domin amincewa da shi kafin ya zama dokar kasa.

Sai dai ya zuwa yanzu babu tabbacin cewar gwamnatin Fira Minista Pedro Sanchez, na da yawan ’yan majalisar da za su goyi bayan kudurin a zauren majalisa.

Duk da matsayin Ministar Daidaita Tsakanin Jinsi, Irene Montero, cewa dokar ta dauki matsayi a kan matsalar da aka dade ana boyewa a shekarun baya.

Ya zuwa wannan lokaci kasashen Koriya ta Kudu da Indonesiya ne kawai ke ba da irin wannan hutu ga mata saboda matsalar al’ada a duniya.