✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za A Fara Biyan ’Yan Fansho N12,000 A Jigawa

Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya amince a fara biyan ’yan fansho mafi karancin albashin N12,000 duk wata.

Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya amince a fara biyan ’yan fansho mafi karancin albashin N12,000 duk wata.

Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Hussain Ali Kila, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis.

Ya ce gwamnatin za ta rarraba wa masu ruwa da tsaki sanarwar amfani sabuwar dokar, domin fara aiwatarwa daga watan Janairun 2023.

Kafin wannan sabon tsarin dai, ana biyan ’yan fanshon N5,000 ne a matsayin mafi karancin albashi.