✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara daukar fasinjoji kyauta a motocin ‘Kanawa Bus’

Gwamnatim Kano ta dauki matakin ne sakamakon rashin tsabar kudi da ’yan Najeriya ke fama da shi

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin fara jigilar fasinjoji kyauta a Motocin Kanawa Bus da gwamnatin jihar ta samar daga ranar Litinin.

Sanarwar hakan ta bulla ne ta shafin Facebook na babban mai ba shi shawara a bangaren kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim, dauke da sa hannun Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, inda ya ce matakin ya biyo bayan rashin tsabar kudi da ake fama da shi a kasar.

Wannan mataki na zuwa ne bayan dokar sauya takardun N1,000, N500 da kuma N200 ta haifar da karancin tsabar kudi a hannun ’yan Najeriya.

Tun a watan Nuwamba ne dai da Gwamnatin Jihar Kano ta kirkiri dokar hana baburan a daidaita Sahu bin wasu manyan hanyoyi, ta kuma samar da manyan motocin da kuma kanana na taksi don jigilar fasinjoji.

Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ce ta fitar da sanarwar, tare da barazanar daukar mataki kan duk wanda ya saba dokar, sai dai zanga-zanga da koke-koken al’umma ya sanya dokar ba ta dore ba.