✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara daure barayin akwatin zabe shekara 20

Dokar ta kuma tanadi daurin shekara 10 kan mai sayar da katin zabensa

Majalisar Dattijai ta amince da kudurin da ke neman a kafa Hukumar Hukunta Laifukan Zabe, ciki har da daure masu satar akwatin zabe shekara 20 a gidan yari.

Hakan dai ya biyo bayan amincewa da rahoton da kwamitin Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya yake jagoranta a zauren Majalisar ranar Talata.

Sanata Gaya, yayin gabatar da rahoton ya ce kafa hukumar ya zama wajibi la’akari da karancin hurumin da INEC take da shi wajen gurfanar da masu aikata laifukan zabe kamar yadda sassa na 149 da na 150(2) na Dokar Zabe ta kasa wacce aka yi wa kwaskwarima suka tanada.

Ya ce INEC kan fuskanci kalubale matuka wajen shiryawa da kuma gudanar da sahihin zabe, sannan kuma ta gurfanar da masu aikata laifi a yayin zaben.

Ayyukan sabuwar hukumar dai za su hada da bincike kan laifukan zabe a Najeriya, gurfanar da masu aikata su a gaban kotu da kuma adana bayanansu.

Dokar ta kuma tanadi hukuncin daurin shekara biyar ko tarar Naira miliyan 10 ga duk jami’in zabe ko kungiya ko jam’iyyar da aka samu da hannu a magudin zabe.

Kazalika, Majalisar ta amince da shawarwarin kwamitin wajen daure duk wanda aka samu da hannu a satar akwati shekara 20 a gidan yari, ko yin amfani da katin zabe ba bisa ka’ida ba, ko buga kundin rijistar masu zabe ba bisa ka’ida ba ko kuma fitar da sakamakon zabe ta kowacce fuska ta bayan fage.

Dokar ta kuma tanadi hukuncin daurin shekara 10 ga dukkan wanda ya sayar da katin zabensa ko aka same shi da katin wani, ko kuma aka kama shi yana kokarin buga kundin rijistar masu zabe.

Majalisar ta kuma tanadi hukuncin daurin shekara 15 kan duk jami’in shari’a ko ma’aikacin kotun da ya yi yunkurin sauya sakamakon zabe.

Ta kuma tanadi daurin shekara 15 ko tarar miliyan 30 kan duk jami’in tsaron da ma’aikatan INEC suka yi kokarin yin amfani da shi wajen tafka magudin zabe.