✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara farautar masu tayar da zaune-tsaye a Jos

Gwamnatin Filato ta sha alwashin maganin masu tada zaune-tsaye.

Jami’an Tsaro a Karamar Hukumar Jos ta Arewa sun bayyana cewar za su fara simamen wanda suke kaiwa jama’a hari ba gaira ba dalili.
Jami’an cikin wata sanarwar da suka fitar a ranar Lahadi, sun bayyana cewar ba sani ba sabo za su zakulo duk wani mai laifi tare da gabatar da shi gaban hukumar don fuskantar hukunci na shari’a.
Wannan na zuwa ne bayan harin da aka kai kan Fulani matafiya a yankin Gada-Biyu da ke kan titin Rukuba a ranar 14 ga Agustan 2021, a karamar hukumar Jos ta Arewa, a Jihar Filato.
Matakin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Kwamitin Zartarwa na Karamar Hukumar Jos ta arewa, Shehu Bala Usman, bayan sassauta dokar hana fita da gwamnatin Filato ta sanya a makon da ya gabata.
Kazalika, kwamitin ya bayyana cewar gwamnatin Simon Lalong ta kashe makudan kudade wajen tabbatar da yanayi mai wanzuwa don samun zaman lafiya mai dorewa a jihar.
Sannan ya ce gwamnatin jihar ta ce ba za ta lamunci duk wani kokari daga wasu bata-gari ba na ruguza yunkurin da ta ke yi na samar da zaman lafiya.
Ya kuma roki sarakunan gargajiya, shugabannin matasa, kungiyoyi masu zaman kansu da daidaikun mutane da ke kishin jihar da su taimaka wa gwamnati wajen bada rahoton duk wanda suke yunkuri tada zaune tsaye.