✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara horas da ’yan sandan da za su maye gurbin SARS

Shugaban ’Yan Sanda ya ce a makon gobe za a fara horas da jami’an sashen da zai maye gurbin SARS

Shugaban ’Yan Sandan Najariya, Mohammed Adamu ya ce za a fara horas da jami’an sashen da zai maye gurbin SARS da aka rusa.

Mohammed Adamu ya bayyana haka ne a lokacin da shahararren mawaki, David Adeleke wato Davido ya ziyarce shi kan zanga-zangar #EndSARS.

“Mun amince akwai babbar matsalar rashin yarda amma muna yin bakin kokari wurin magance ta”, inji shi.

Ya kara da cewa, “Mun rushe SARS saboda haka muna son masu zanga-zanga su kwantar da hankali su ba lokaci mu magance matsalar wanda za a yi tare da ’yan kasa.

“Yadda na yi magana da kai, zan ci gaba da ganawa da sauran masu tsaki in kuma tuntubi kungiyoyin kare hakki su bayar da gudunmuwa kan sabon sashen da za a kafa”.

Ya ce za a biya diyya ga iyalen wadanda karfa-karfar SARS ya ritsa da su bayan an kammala bincike.

Bayan ganawar, Davido ya tabbatar wa ’yan jarida cewa shugaban ’yan sandan ya ba shi izinin kafa kwamiti mai zaman kansa da zai lura da sake horarwa da kuma sauya wa jami’an SARS wuraren aiki.