✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a fara nuna gasar Firimiyar Najeriya kai tsaye

Hukumar Shirya Gasar Firimiyar Najeriya (LMC) ta sanar da cewa za a fara nuna wasannin gasar Firimiyar Najeriya kai tsaye a talabijin. Za a rika…

Hukumar Shirya Gasar Firimiyar Najeriya (LMC) ta sanar da cewa za a fara nuna wasannin gasar Firimiyar Najeriya kai tsaye a talabijin.

Za a rika nuna wasannin ne a tashar NPFL.tv, inda za a iya kallo ta waya a ko’ina a fadin duniya.

Za a fara amfani da tashar ce a wasanni na biyu bayan gwajin da aka yi a wasannin farko.

A wasannin farko, an nuna dan wasan Super Eageles Simon Moses yana kallon wasan Firimiyar Najeriya a gida yana zaune a wayarsa.

Wannan yana daya daga cikin nasarorin da ake samu wajen ciyar da gasar gaba.