✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a fara rajistar masu hawa keke a Zamfara

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa za ta fara yi wa masu hawa keke a Jihar Zamfara.

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) za ta fara yi wa masu hawa keke rajista a Jihar Zamfara.

Kwamandan hukumar a jihar, Iro Danladi, ya ce rajistar ababen hawa musamman ma kekuna, na da matukar muhimmanci a wannan gabar domin tantance mahayansu, sakamakon matsalar tsaron da jihar ke fuskanta.

Ya ce hakan zai taimaka wa hukumar rage yawan masu karya ka’idojin titi, zai dafa wajen dakile tabarbarewar tsaro a jihar.

Kwamandan ya bayyana hakan ne yayinkarbar shugabannin Kungiyar NUJ reshen jihar a ofishinsa da ke Gusau ranar Talata.

Ya ce a sauye-sauye da hukumar za ta yi za sy hada guiwa da ’yan jaridar domin wayar da kan al’ummar jihar domin ta haka ne kadai shirye-shiryen za su samar da nasarar da ake bukata.

A nasa banagren, shugaban kungiyar Ibrahim Maizare, ya yi kira ga Hukumar da ta samar da wani sashi na musamman da kungiyar za ta iya bada gudummawarta kai tsaye, domin karfafa alaka tsakanin su.