✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wuraren shakatawa a Abuja za su fara rufewa daga karfe 7 na yamma

umarnin zai fara aikin ne daga ranar Litinin

Hukumar Babban Birin Tarayya Abuja ta umarci ilahirin wuraren shakatawar da ke kewayen birnin da su fara rufewa daga karfe 7:00 na yamma a kullum.

Babban Hadimin Ministan babban binin kan duba ayyuka, Ikharo Attah, wanda ya shaida wa manema labarai hakan a karshen mako ya kuma ce umarnin zai fara aiki ne daga ranar Litinin.

Ikharo ya ce, “Hukumar Babban Birnin Tarayya ta yi bayani karara a kan dokar. Jami’in Sashen da ke Kula da Babban Birnin, da kuma Daraktan da ke kula da tashoshin mota da wuraren shakatawa sun fayyace batun.

“Ministan Abuja ya bayar da umarnin cewa dole a fara rufe tashoshin daga karfe 7:00, wannan shi ne abin da dokar ta kunsa.

“Duk tashar motar da ta ki bin umarnin za a hukunta ta.

“Na samu kira daga wasu mutane da ke bukatar su ci gaba da hutawa bayan tashi aiki da daddare, amma na ce a’a.

“Dole su fara koyar bin wannnan dokar har su saba da ita,” inji shi.

Idan za a iya tunawa, a kwanan nan Shugaban Sashen Kula da Raya Birnin (AMMC) na hukumar, Umar Shu’abu, ya umarci tashosin su fara budewa karfe 8:00 na safe sannan su rufe karfe 7:00 na yamma.

Ya ce daukar matakin na cikin irin tsare-tsaren da hukumar ta fito da su a kan tashoshin.

Ikharo ya ce umarnin zai tamaka wa hukumar birnin wajen bibiyar ayyukan tashoshin motar yadda ya kamata.