Daily Trust Aminiya - Za a fara yanke wa masu fyade hukuncin kisa a Jigawa
Subscribe

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa

Za a fara yanke wa masu fyade hukuncin kisa a Jigawa

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, ta amince a fara yankewa tare da zartar da hukuncin kisa da daurin rai-da-rai ga wadanda aka samu da aikata laifin fyade.

Kakakin Majalisar, Idris Garba ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar da aka gudanar a jiya Laraba.

Kudirin da Majalisar ta amince da shi ya tanadi daurin rai-da-rai ga wanda aka samu da laifin fyade da kuma hukuncin kisa ga duk wanda ya gogawa wanda ya yi wa fyaden cutar Kanjamau da wasu ke kira ‘Sida’ wato HIV/AIDS.

Rahoton da jaridar BluePrint ta ruwaito ya ce majalisar ta cimma matakin hakan ne a ranar Laraba bayan amincewa da rahoton kwamitin shari’a wanda ya kunshi mutum bakwai, karkashin jagorancin Abubakar Jallo.

Honarabul Jallo mai wakilta mazabar Hadejia, ya ce mafi karancin diyyar da za a rika biyan wanda aka yi wa fyade ita ce naira dubu dari biyar doriya a kan hukuncin da kotu za ta yanke wa wanda aka samu da aikata laifin.

Kafatanin ’yan majalisar 30 da ke wakiltar Kananan Hukumomi 27 na jihar sun amince da kudirin, inda za a mika wa Gwamna Muhammad Badaru domin rattaba hannu gabanin ya zama doka a jihar.

More Stories