✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa a Filato – Lalong

Gargadin dai ba ya rasa rasa nasaba da karuwar garkuwa da mutane a Jihar.

Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya gargadi masu garkuwa da mutane cewa duk wanda aka kama a Jihar zai fuskanci hukuncin kisa.

Gwamnan ya yi maganar ne a cocin Cathedral da ke Karamar Hukumar Shendam ta Jihar.

Ya kara tabbatar wa da mutanen Jihar cewa gwamnati za ta kara karfafa fadan ta kan dukkan miyagun laifuka, musamman garkuwa da mutane wanda ya zama babban kalubale ga kwanciyar hankali da tsaron mutane.

Ana ganin gargadin na Gwamnan ba ya rasa nasaba da yawan garkuwa da mutane da aka fuskanta a wasu sassa na Jihar ba.

Ko a ranar 26 ga watan Disamban 2021, Aminiya ta arwaito yadda aka dauke Mai Garin Gindiri da ke Karamar Hukumar Mangu, daga baya suka sake shi bayan ya shafe kwana hudu a hannunsu yana tsare.

Kazalika, a ranar jajiberin sabuwar shekara ma, an dauke wani tsohon dan takarar Gwamna a Jam’iyar PDP, Dr Kemi Nshe, daga gidan shi da ke yankin Shendam.