✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fuskanci hazo da kurar da za su iya hana jirage tashe a Arewa – NiMet

NiMet ta shawarci masu amfani da hanyoyi da ma masu matsalolin numfashi su yi taka-tsantsan.

Hukumar Kula da Harsashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar a fuskanci hazo da kura masu tsananin gaske a wasu sassa na Arewacin Najeriya daga ranar Asabar.

Hukumar ta kuma yi gargadin cewa yanayin na iya hana jirage sauka da tashi a wasu sassa na yankin.

NiMet dai ta shawarci masu amfani da hanyoyi da ma masu matsalolin numfashi da su yi taka-tsantsan.

A cikin wata sanarwa da Babban Sashen Harsashe (CFO) na hukumar ya fitar ranar Asabar, NiMet ta ce daga yammacin ranar ta Asabar ake sa ran yanayin zai fara canzawa a garuruwan.

“Akwai wata sabuwar kura tana nan ta taso daga yankin Faya Largeau da ke kasar Chadi. Ana sa ran za ta shigo Najeriya, kuma za ta kai ga disashe yanayi,” inji hukumar.

Sanarwar ta ce ana sa ran ci gaba da ganin hazon da kurar tun daga yammacin na Asabar har zuwa kwanaki biyu masu zuwa a akasarin sassan Arewacin Najeriya.

Garuruwan da yanayin zai fi shafa a cewar NiMet su ne Maiduguri da Yobe da Nguru da Potiskum da Dutse da Gombe da Yola da Bauchi da Katsina da Kano da kuma Kaduna.

Hukumar ta kuma ce akwai yiwuwar a soke sauka da tashin wasu jirage, inda ta shawarci kamfanonin sufurin jiragen sama da su kiyaye da yanayin.