✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta gina filin jirgin sama na 2 a Legas

Gwamnatin Legas za ta gina wani sabon filin jirgin sama a yankin Lekki, wanda zai zama filin jirgi na biyu a jihar

Gwamnatin Legas za ta gina wani sabon filin jirgin sama a yankin Lekki, wanda zai zama  na biya a jihar bayan filin jirgi  na Murtala Mohammed.

Kakaki na musamman ga gwamnan jihar, Ope George, ya ce Gwamnatin Babajide Sanwo-Olu ta samu amincewar Gwamnatin Tarayya kan gina sabon filin jirgin a jihar.

Batun gina filin jirgin saman jihar ya tsaya cik tsawon shekaru, tun lokacin da aka gabatar da ia a zamanin gwamnatin tsohon Gwamna Babatunde Fashol.

A lokacin an tura wa masu zuba jari a fadin duniya takardun bukatar su zuba jari a aikin filin jirgin da aka kiyasta zai lakume Dala miliyan 450 a lokacin.

An tsara aikin gina filin jirgin ne a matsayin hadin gwiwa tsakanin ’yan kasuwa da gwamnatin jihar, wadda za ta samar da filin da sauran kayan more rayuwa.

A daya bangaren kuma, masu zuba jari daga ciki da wajen Najeriya, za su gina filin jirgin a karkashin tsari mai gamsarwa kuma daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya.

A baya wasu manyan kamfanonin kwararru hudu sun yi aiki tare da Gwamnatin Jihar Legas a matsayin masu ba da shawara kan aikin filin jirgin.

Sai dai duk da haka ba a aiwatar ba, sai yanzu da Gwamnatin Sanwo-Olu ke shirin aiwatarwa da zummar filin zai karbi fasinjoji milian biyar a shekara.

Hadimin gwamnan ya ce aikin da ake sa ran za a fara a shekarar 2023, za a gina shi ne a kan fili mai fadin kadada 3,500, kuma tuni an riga an kammala zanen tsari da na’urorin jiragen sama.

A gefe guda kuma ana ci gaba da nazari kan dabaru, yadda za a samu kudade da sauran batutuwa, wadanda bayan su za a fara batun kasuwanci.