✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a gina shagunan zamani 500 a Kasuwar Kantin Kwari

Gwamnatin Jihar Kano ta kulla yarjejeniya da wasu kamfanoni masu zaman kansu a jihar don sake gina shagunan zamani kimanin guda 500 a Kasuwar Kantin…

Gwamnatin Jihar Kano ta kulla yarjejeniya da wasu kamfanoni masu zaman kansu a jihar don sake gina shagunan zamani kimanin guda 500 a Kasuwar Kantin Kwari da ke jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa kamfanonin da ake sa ran za su gudanar da wannan aiki karkashin tsarin aikin hadin gwiwa tsakanin ‘yan kasuwa da gwamnati sun hada da kamfanin gine-gine na Razz da takwaransa na Unikues.
Za a gina sabbin shagunan ne a manyan filayen da ke kasuwar ta bangaren Plaza da kuma ta bangaren Filin Pakin. A lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan sanya
hannun a takardar yarjejeniyar Kwamishinan Ma’aikatar kasa da
Tsare-Tsare Alhaji Faruk B.B. Faruk ya bayyana cewa gwamnatin ta fito da wannan aiki ne don bunkasa tattalin arzikin jihar tare da  inganta harkokin ‘yan kasuwa a jihar.
A cewarsa aikin zai lashe kudi kimanin Naira miliyan dubu 244. Kuma ‘yan kwangilar ne za su aiwatar da ginin da kudinsu ba tare da ko kwabon gwamnati ba.
“Wannan sabon tsari ne wanda ba da kudin gwamnati za a yi aikin ba, ’yan kwangilar ne za su aiwatar da aikin da kudinsu. Idan sun gama aikinsu a karshe gwamnati za ta amfana da wasu shaguna da darajarsu za ta kai Naira miliyan dari uku. Hakazalika, su ma ‘yan kasuwa an samar musu da shaguna don gudanr da kasuwancinsu cikin jin dadi haka su ma kananan ‘yan kasuwa za samu gyararren wurin da za su samu damar kasa kayansu. Wannan tsari ne da ake yi a kasashen duniya inda masu kudi za su sa jarinsu su yi aiki wanda zai zama mai amfani ga su akansu da kuma gwamnatin,” inji shi.
Kwamishinan ya yi kira ga ‘yan kwangilar da su yi aikin bisa inganci tare da kammala shi a kan lokaci na tsawon shekara guda.
Da yake mayar da jawabi Manajan Daraktan Kamfanin Razz Alhaji Sani Lawan Attana a madadin kamfanonin guda biyu ya yi alkawarin cewa za su yi aiki dare da rana don ganin sun aiwatar da aikin cikin wa’adin da gwamnatin ta diba musu.