✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a gudanar da zabe kamar yadda aka tsara —Majalisar Tsaro

Zaben zai gudana duk da ‘yan matsalolin da ake fuskanta nan da can.

Majalisar Tsaron Najeriya ta ce babu abin da zai hana gudanar da zaben Shugaban Kasa da kuma ‘yan Majalisar Tarayya a ranar Asabar mai zuwa kamar yadda aka tsara, duk da ‘yan matsalolin da ake fuskanta nan da can.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya shaida wa manema labarai haka bayan wani taron da majalisar ta gudanar wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a wannan Larabar.

Aminiya ta ruwaito cewa an gudanar da taron domin karbar bayanai daga Hafsan Hafsoshin sojin kasar, Janar Lucky Irabor da shugabannin rundunonin sojin sama da kasa da ruwa tare da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Baba Alkali.

Malami ya ce bayan gamsuwa da bayanan da shugabannin hukumomin tsaron suka gabatar, majalisar ta ba da umurnin ci gaba da shirin zaben kamar yadda aka shirya a ranar 25 ga wata, kamar yadda Majalisar Zartarwa da majalisar bada shawara ta tsoffin shugabannin kasa suka bada umurnin.

Ita ma Hukumar Zaben kasar INEC ta ce ta shirya tsaf domin ganin an gudanar da zaben kamar yadda doka ta tanada.

Za a fara da zaben Shugaban Kasa da Majalisar Tarayya, kana a biyo da na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan gobe.