✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za A Haramta TikTok A Ma’aikatun Amurka

Majalisar Dattawa ta amince da haramta amfani da kafar sada zumunta ta TikTok a na’urorin gwamnatin Amurka

Majalisar Dokokin Amurka ta amince da kudirin dokar haramta amfani da kafar sada zumunta ta TikTok a ma’aikatun gwamnatin kasar.

A ranar Juma’a Shugabar Majalisar Tarayya ta kasar, Nancy Pelosi, ta bayyana goyon bayanta ga kudurin, wanda Majalisar Dattawa ta riga amince da shi a matsayin doka.

Nancy Pelosi ta goyi bayan sanya matakin ne a cikin dokar haramta wa ma’aikata amfani da TikTok a kan na’urorin Gwamnatin Tarayya.

Wannan zai kasance wani bangare na dokar kudin kasar wadda Majalisar Wakilan da Pelosi take jagoranta za ta yi zama a kai a mako mai kamawa.

Bisa dukkan alamu haramcin TikTok, wanda mallakin wani kamfanin kasar China ne, zai zama doka ganin yadda babban dan Majalisar daga Jam’iyyar adawa ta Republican, Kevin McCarthy, ke goyon bayan hakan kai da fata.

A ranar Laraba kudurin dokar haramta amfani da kafar TikTok ta na’urorin gwamnati ta samu amincewar Majalisar Dattawan kasar.

Wannan shi ne mataki na baya-bayan nan da majalisar kasar ta dauka bisa zargin cewa China, wadda ke zaman doya da manja da Amurka, na iya amfani da kamfanoninta wajen yin  leken asiri a kan Amurkawa.

Amma kamfanin TikTok ya ce ba komai ba ne ya haifar da fargabar illa farfaganda da labaran karya da ake yadawa.

Sai dai dokar ba za ta haramta wa Amurkawa sama da miliyan 100 da a halin yanzu suke amfani da TikTok ci gaba da yin hakan a kan na’urorinsu ko a kamfanoni masu zaman kansu ba.