✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a hukunta dan sanda saboda sakaci da aiki a Gombe

An samu jami'in da sakaci na barin wasu masu laifi har suka tsere.

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Baba’ita, ya sa a hukunta wani jami’insa bayan samunsa da laifin sakaci da aiki.

An dauki wannan mataki wanda kwamishinan ya bayyana a matsayin abun takaici kan yadda jami’in ya bari wasu masu laifi da suke tsare suka tsere a garin Kamo Tungo Awak da ke Karamar Hukumar Kaltungo ta jihar.

Bayanai sun ce an kama batagarin ne bisa zarginsu da laifin fasa shagunan mutane a kokarinsu na kwasar dukiya.

Sai dai a cikin wata takarda da Kwamishinan ‘Yan sandan ya aike wa manema labarai ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce al’ummar garin ne suka yi kokari suka kama matasan sannan suka damka su a hannun ‘Yan sanda amma sai aka wayi gari sun gudu.

ASP Mahid Mu’azu  ya ce irin wannan ganganci da sakaci da aiki da jami’in dan sanda da ke bakin aiki ya yi har masu laifin suka gudu ce ta sa Kwamishinan ya samar da motar sintiri da jami’an tsaron sirri suka dukufa aiki.

Ya ce wannan ci gaba ne ya yi tasiri har aka kamo guda uku da suka tsere inda kuma ake ci gaba da neman ragowar biyun.

Ya ci gaba da cewa wadanda aka kamo din tuni aka mayar da su sashen binciken manyan laifuffuka na SCID a shelkwatar hukumar da ke Gombe domin ci gaba da gudanar da bincike a kai.