✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara hukunta mara sa amfani da takunkumi a Kano

“Mun san dole mutane za su yi korafi, amma hakan ba zai hana mu yin abinda ya dace ba."

A cikin irin matakan da take dauka domin yaki da sake dawowar annobar COVID-19, Gwamnatin Jihar ta ce ta ce za ta kafa kotunan tafi-da-gidanka domin hukunta mara sa amfani da takunkumi nan ba da jimawa ba.

Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da hakan yayin wani taro na masu ruwa da tsaki a jihar, wanda ya gudana da masu asibitoci masu zaman kansu a Fadar Gwamnatin Jihar ranar Asabar.

Ganduje ya ce, “Nan ba da jimawa ba, za mu kafa kotunan na tafi-da-gidanka wadanda za su taimaka mana wajen tabbatar da ana amfani da takunkumin rufe fuska a jihar Kano.

“Mun san dole mutane za su yi korafi, amma hakan ba zai hana duk wata gwamnatin da ta san ya-kamata daga yin abinda ya dace ba.

“Ba za a dauke hankulanmu daga yin abinda ya dace ga jama’ar mu ba, wannan hadin gwiwar a tsakaninmu zai ci gaba,” inji Gwamnan.

Daga nan sai ya kuma yi kira ga al’ummar jihar kan su ci gaba da kiyaye matakan kariya daga cutar, musamman wajen amfani da takunkumin, wanke hannuwa, bayar da tazara da kuma amfani da sinadarin tsaftace hannuwan.

A wani labarin kuma, Gwamnatin Jihar ta ta kuma rabawa asibitocin masu zaman kansu dake jihar kyautar kayan kariya daga cutar kimanin guda 2,000 da kuma takunkumi 100,000.

Gwamnatin ta ce ta yi hakan ne domin ta taimaka musu su wajen kula da lafiyar ma’aikatan wadanda sune a kullum suke cudanya da masu dauke da cututtuka.