✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a iya magance rikicin Boko Haram a siyasance – Zulum

Ana iya yin amfani da matakan siyasa wajen magance rikicin Boko Haram, cewar Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce za a iya magance rikicin ku giyar Boko Haram ta hanyar siyasa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan ya tattauna da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

A yayin ganawar Gwamnan da shugaba Buhari kan kalubalen tsaron da jihar ke fuskanta, ya ce “Tunkarar matsalar da karfin tuwo ba zai magance matsalar ba duka.”

Zulum ya bukaci dukkan matakan gwamnatoci da su samar wa da matasa ayyukan yi don kaucewa masu samun damar shiga gonakin jama’a su aikata sace-sacen amfanin gona.

Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da cewa jama’ar jihar da suke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira sun koma garuruwansu domin su ci gaba da yin noma a gonankinsu da kuma rayuwa kamar yadda suka saba.