✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za a iya raba mutum miliyan 100 da talauci nan da 2025’

Tilas ne shugabanni da kasashe su mike wajen dakile abubuwan da suke haddasa talauci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce za a iya fitar da mutum miliyan 100 a fadin duniya daga kangin talauci nan da shekarar 2025.

Majalisar ta ce duk da barazanar koma-bayan tattalin arziki da ake fuskanta, abu ne da zai yiwu a raba mutum miliyan 100 da talauci nan da shekarar 2025.

Sakamakon binciken da majalisar ta fitar kan taulaci, ya nuna za a iya rage talaucin da ake fama da shi, a kuma samar da sababbin dabaru a fagen yaki da talaucin don taimaka wa gwamnatoci wajen cimma wannan kudiri.

Majalisar ta fitar da sakamakon binciken ne a Ranar Yaki da Talauci ta Duniya, wadda akan yi ran 17 ga Oktoban kowace shekara.

Ta ce, domin cim ma nasara a wannan yaki, tilas ne shugabanni da kasashe su mike tare da daukar ingantattun matakan dakile abubuwan da suke haddasa talauci a cikin al’umma.