✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kaddamar da tashoshin kashe gobara a kasuwannin Najeriya

An samu tashin gobara a akalla kasuwanni hudu na Arewa a bayan nan.

Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS) ta ayyana shirinta na kaddamar da tashoshin kashe gobara a kasuwanni a fadin kasar.

Shugaban Hukumar mai kula da shiyyar Kano da Jigawa, Mataimakin Kwanturola Janar (ACG), Ahmed Garba-Karaye, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Kasuwar Singa domin duba irin barnar da gobarar ta yi a ranar Litinin a Kano.

Ya bayyana cewa hukumar ta himmatu wajen dakile aukuwar gobara da kuma shawo kan gobarar idan tsautsayi ya sa ta auku.

A cewarsa, bincike ya kankama domin nazari tare da tabbatar da bin ka’idodin kashe gobara a gine-ginen jama’a.

Ya bayyana cewa, “ana samun karuwar aukuwar gobara a kasuwannin Kano sakamakon yanayin zafi da kuma rashin ingancin kayayyakin lantarki.

“Tsananin zafi da ake fama da shi hadi da dumamar yanayi sanadiyyar amfani da man fetur da dangoginsa a matsayin makamashi, suna daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da tashin wuta cikin gaggawa.” in ji shi.

Garba-Karaye ya kara da cewa, ya kamata a rika rage cunkuso domin samun wadatacciyar iska da za ta rika ratsawa a cikin shaguna, kasancewar zafi na iya kara haddasa gobara.

Ya bukaci shugabannin kasuwa da su dage wajen fadakar da sauran ’yan kasuwa ta hanyar alamu da sanarwa a kan muhimmancin kashe kayan lantarki gabanin rufe wurarensu na kasuwanci.

Garba-Karaye ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su bayar da gudunmawarsu a bangaren samar da kayan aikin kashe gobara.

Ya shawarci ’yan kasuwa da su kasance cikin shirin ko ta kwana na aukuwar gobara a koda yaushe.

A bayan nan, an samu aukuwar gobara a wasu kasuwannin Arewa da suka hada Kasuwar Rimi ta Kano, Kasuwar Monday a Borno da kuma Kasuwar Gamzaki a Adamawa.

(NAN)