✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a kafa cibiyoyin fasaha 6 don bunkasa tattalin arzikin Najeriya

Gwamnati ta ce cibiyoyin za su taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa cibiyoyin fasaha fa kirkira guda shida a kasar nan domin bunkasa tattalin arziki.

Za a kafa cibiyoyin ne a dukkan shiyyoyin siyasa guda shida na Najeriya domin cike gibin da ke tsakanin makarantu da cibiyoyin bincike a hannu daya, da kuma masana’antu a daya gefen.

Ministan Kimiyya da Fasaha, Dokta Ogbonnaya Onu ne ya bayyana hakan a Kano lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje a Gidan Gwamnatin Jihar ranar Litinin.

A cewarsa, “Akwai bukatar mu sana’antar da binciken da ake yi a manyan makarantunmu a matsayin hanyar da za mu bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu, mu rage shigo da kaya da samar wa da matasa ayyukan yi.

“Fatanmu shi ne wadannan cibiyoyin za su taka muhimmiyar rawa wajen ganin kayan da Najeriya take sarrafawa sun yi kafada da kafada da takwarorinsu na kasashen duniya, ko ma su fi su.

“A yankin Arewa maso Yamma, za mu kafa wannan cibiyar a Jihar Kano la’akari da matsayinta na cibiyar cinikayya a Arewacin Najeriya da kuma zaman lafiyan da take da shi,” inji Dokta Onu.

Ministan ya kuma ce yunkurin ya zo daidai da kudurin gwamnati mai ci na zakulo mutum miliyan 100 daga talauci cikin shekara 10.

Ya kuma ce idan shirin ya sami nasara, hatta darajar Naira zai farfado sakamakon rage shigo da kaya daga kasashen waje da kuma fitar da namu.

Da yake nasa jawabin, Gwamna Ganduje ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan kirkiro shirin tare kuma da zaben Jiharsa domin gina cibiyar a Arewa maso Yamma.

Kano dai ita ce Jiha ta farko da aka kaddamar da shirin kuma nan ba da jimawa za a karade sauran sassan kasar.