✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kai Murja Ibrahim gwajin kwakwalwa

’Yan sanda sun ce sai an kammala gwajin, za a ci gaba da binciken matashiyar da ke tashe a kafar Tiktok

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ba da umarnin yi wa fitacciyar mai amfani da shafin sada zumuntar nan na TikTok a Jihar, Murja Ibrahim, gwajin kwakwalwa domin gano ko tana da tabin hankali.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mamman Dauda, ne ya bayar da umarnin, a cewar Kakakin rundunar a Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Kakakin ya ce sai an gudanar da gwajin ne za a ci gaba da bincike kan kamun da ’yan sanda suka yi mata.

Idan za a iya tunawa, Aminiya ta rawaito muku yadda ’yan sanda suka kama Murja ranar Lahadi, bayan sun karbi korafi a kan yadda take amfani da shafin wajen zage-zage da kuma bata tarbiyya.

An kama ta ne a otal din Tahir Guest Palace da ke Kano, tana tsaka da shirye-shiryen gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarta.

Majalisar Malamai ta Jihar Kano ce dai ta kai korafi kan Murja bisa yadda ta ce bidiyoyin da take wallafawa a shafin nata sun saba wa koyarwar addinin Musulunci.

Sai dai daga bisani ta yi alkawarin cewa daga yanzu ta daina zage-zagen kamar yadda aka bukata.

Kamun nata dai ya janyo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke kiran da a gaggauta sarkinta, wasu kuma na cewa ya zama wajibi a hukunta ta don ya zama izina ga wasu.